Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tashin kuɗin yin bahaya ya janyo damuwa a Kano
- Marubuci, Daga Zahraddeen Lawan a Kano da Umar Mikail a Abuja
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Wasu mazauna birnin Kano da ke arewacin Najeriya, na bayyana damuwa a kan ƙarin kuɗin shiga gidan wanka da bahaya, wanda ya kai kusan kashi 70 cikin 100 a baya-bayan nan.
Lamarin na zuwa ne, daidai lokacin da ake kokawa kan hauhawar farashin kaya da na ayyuka, sanadin cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar darajar naira a kasuwar canji.
Mutane kan shiga gidajen wanka ne don yin ba-haya ko wanka da wanki da kama-ruwa ko fitsari, kai har ma da alwala.
Sai dai, masu gidajen wanka a Kano yanzu duk sun ƙara kuɗaɗen waɗannan muhimman buƙatun rayuwa, yayin da tashin farashin yin bahaya da kama-ruwa ko fitsari, ya fi tayar da hankula, saboda kasancewar sa buƙatar da ta zama dole.
Tuni wasu mazauna Kano, suka shaida wa BBC cewa ala dole, sun fara ɗaukar matakin rage shiga gidan wanka, saboda tashin farashin.
Ɗumbin mutane ne a birnin, mai cunkoson jama'a suka dogara da irin waɗannan gidajen bahaya da ake biyan kuɗi, don biyan buƙatun rayuwa na yau da kullum.
Alƙaluma daga Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) sun nuna cewa hauhawar farashin ta kai kashi 24.08 cikin 100 a watan Yulin 2023, daga 22.79 da aka samu a watan Yunin shekarar.
Akasari akan gina banɗakunan haya waɗanda ake kira gidan wanka a kasuwanni da wuraren taruwar jama'a a Kano, jihar da ke da mafi yawan jama'a a Najeriya. Wani rahoton NBS na 2020 ya ce yawan al'ummar jihar ya kai mutum 14,253,549.
Ana fargabar akwai yiwuwar ƙarin kuɗin ba-hayar ya ƙara ta’azzara matsalar yin ba-haya a fili, kasancewar wasu ko da suna da kuɗin da za su biya ba za su yi hakan ba, sun gwammace su yi a waje, saboda matsin rayuwa.
Wani rahoton Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya - Unicef - da ya fitar a watan Yulin 2023 ya ce sai Najeriya ta gina banɗaki kusan miliyan hudu a duk shekarakafin ta iya kawar da matsalar yin ba-hayar a sarari nan da shekara ta 2025.
'Ƙarin ya sa na rage shiga gidan wankan'
Babu tabbas game da yawan gidajen wankan da ke faɗin Kano, amma dai ana iya cewa akwai ire-irensu a dukkan kasuwannin cikin birnin.
Sai dai duk da irin muhimmancin da banɗakin ke da shi a rayuwar ɗan Adam, wasu sun gwammace su rage shiga saboda ƙarin kuɗin.
"Na rage shiga saboda ƙarin ya yi yawa, ina zuwa sau uku ko huɗu a rana," kamar yadda wani da bai amince ya bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC.
Ya ce a baya yakan biya naira 50 amma yanzu an ce masa sai ya biya 70.
"A hakan ma nan ɗin ya fi wasu wuraren sauƙi. Duk da haka dai wani lokacin sai an yi mani alfarma."
Wani mutumin daban kuma wanda muka ɓoye sunansa, ya ce sun yarda da ƙarin ne saboda tashin farashin kayayyaki.
"A yanzu N50 muke biya idan za a yi ba-haya, amma da bai kai haka ba. Shi ma fitsari a da N5 ne ko kuma kyauta, amma yanzu N10 ne," in ji shi.
Dalilin da ya sa muka ƙara farashi - Masu gidan wanka
A gefe guda kuma, masu gidajen wankan na cewa dole ce ta sanya su ƙara kuɗin ba-haya da na wanka saboda kuɗaɗen kayan da suke amfani da su - kamar sabulu da abubuwan tsaftace bayan gida - sun yi tashin gwauron-zabi.
Misbahu Zakariyya mai gidan wanka ne a bakin Kasuwar Kantin-Kwari, kuma ya ce dalilan da suka jawo ƙarin suna da yawa.
"Akwai sabulun da muke saya N140 zuwa N150, yanzu ya koma N600," a cewarsa. "Man shafawa da muke saya N200 ya koma N700.
"Muna sayen buhun soso [na wanka] N1,500, yanzu ya koma N8,000 zuwa 9,000. Ka ga dole a yi ƙari."
Misbahu ya ƙara da cewa baya ga tsadar kaya, akwai kuma kuɗin haya da masu gidajen wankan ke ƙara musu, wanda suke biya duk wata.
"Kamar ni, gidan wankan ba nawa ba ne, an ba ni ne don na dinga biyan kuɗi duk wata. Wani zubin kuma sai ka ji iyayen gidan sun ce sun yi ƙari. Ga kuɗin ruwa da muke biya duk wata saboda ba mu da rijiyar burtsatse."
Tsuguno a fili na kashe dubun dubatar yara
A Najeriya, ƙananan hukumomi 93 ne kawai cikin 774 asusun Unicef ya saka su cikin tsarin Open Defecation Free - wato wuraren da aka daina yin ba-haya ko fitsari a fili.
Kazalika, rahoton Unicef ɗin na watan Afrilun 2023, ya ce mutum miliyan 17 ne ke yin ba-haya ko fitsari a fili a faɗin Najeriya.
Bugu da ƙari, yara kusan 900,000 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon cutukan da ke da alaƙa da rashin tsafta, a cewar asusun.