Me ke kawo gurɓacewar iska a Kano?

Birnin Kano daya daga cikin manyan biranen Najeriya na fuskantar gurbacewar iska mafi muni da ba a taba gani ba a tarihi.

Gurbacewar ta zarce mizanin da hukumar lafiya ta duniya ta kayyade na mafi muni a cikin awa ashirin da hudu da za a iya samu.

Wannan al'amarin na haddasa larurar numfashi da zuciya ga wasu mutane.

A ‘yan kwanakin nan ana fama da tsananin zafi da kadawar iska mai zafi a sassan birnin na Kano wanda ya kasance cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Abubuwa da dama ciki har da karuwar al’umma da gine-gine ba bisa ka’ida ba da masana'antu masu fitar da mummunar iska da uwa-uba rashin bishiyoyi sune suke haifar gurbacewar iska a sassan jihar.

Gurbacewar iskar ta kai wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Dr. Dahiru Muhammad Hashim wani likita ne mai yaki da sauyin yanayi a jihar ya ce akwai abin da ake cewa ‘air quality’ wato ingancin iska wanda ke samar da ainihin tsaftatacciyar iska.

Dr Dahiru ya ce kididdigar hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin mafi yawa na gurbatacciyar iska kar ya wuce 53.4 amma a Kano akwai wuraren da suke da ninkin wannan iska fiye da sau goma.

Ko wace irin illa rashin kyakkyawar iska ke haifarwa ga lafiya mutum?

Dr. Dahiru ya kara da cewa tilas dan'Adam ya rayu da bishiyoyi kasancewar suna fitar da iskar da yake bukata, sannan bishiyar kuma, na bukatar iskar da muke fitarwa.

“Na farko shi ne cutukan hanyoyin numfashi; Wasu mutanen da sun shaki gurbatacciyar iska sai su sarke, Sannan akwai matsalolin hawan jini da ake iya kamuwa da su saboda duk lokacin da mutum ya shaki iska maras kyau yana sa wa jini baya guda cikin jikin mutum yadda ya kamata saboda iska ta yi nauyi" a cewar Dr Dahiru.

Masana, sun bayyana cewa babban hanyar kawar da cutukan da suke da alaka da iska da kuma samar da kyakkyawar iska a cikin al’umma, ita ce shuka bishiyoyi da daina kona shara barkatai.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa duk bishiyar da aka shuka ta girma, to za ta iya bai wa mutum hudu iskar shaka.

Me gwamnatin Kano ke yi game da matsalar gurbatacciyar iska?

Dr. Kabir Ibrahim Getso kwamishinan muhalli na jihar Kano ya ce akwai dokoki da gwamnatin kano ta samar da kuma na gwamnatin tarayya ciki har da dokar gurbatacciyar iska wato “air pollution bill” sannan kuma ya ce ma’aikatar tana bin masana’antu don tabbatar da cewa suna kayyade yawan hayaki da iska ko dagwalon da suke fitarwa.

“Akwai shirin dashen bishoyoyi da gwamnatin Kano ke yi duk shekara musamman a lokacin damina a ma’aikatu da unguwanni da wuraren taruwar jama’a inda ake bayarwa kyauta don su dasa" in ji Dr Getso.

Yanzu haka dai bayanai na cewa jama’a na ta kokawa da dan-karen zafin da ake yi a sassan Kano, birni mai yawan mutane da masana’antu, abin da yake nuna bukatar gwamnati da jama’a da sauran kungiyoyi su tashi tsaye wajen shuka bishiyoyi masu yawa da kuma samar da tsarin bin dokokin kyautata muhalli sau da kafa.

Kwararru na cewa bishiyoyi na taimaka wa dan Adam zuke duk wata gurbatacciyar iskar da ba ya bukata tare da samar da ‘ya’yan itatuwa masu taimakawa jiki.