'Yadda aka yaɗa hotunan tsiraicina saboda na karɓi bashi ta intanet'

An yaɗa wasu hotunan mijina tsirara, inda aka haɗa hoton nasa da na wata mace, lamarin bai tsaya a nan ba, sun sake sanya hotunana a wani shafi da bai dace ba.
Sun kuma haɗa da lambar wayata da aka riƙa kira na, ana mini maganar da ba ta dace ba.
Wannan labarin Fawzia ne, wadda mijinta ya ci bashin Rupee 10,000 na ƙasar Pakistan ta hanyar wata manhajar cin bashi ƴan watannin da suka gabata.
Sai dai bayan wani ɗan lokaci, kuɗin sun ninka.
Dalilin haka ne ya sa Fawzia da mijinta sayar da kayan gidansu gaba ɗaya domin su biya bashin.
A wannan lokacin da shafukan sada zumunta ke taka muhimmiyar rawa, ya kamata kowa ya yi taka-tsantsan saboda hotonka zai iya faɗawa hannun mutanen banza, waɗanda za su iya amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.
An riƙa yi wa Fawzia da mijinta barazana ana karɓar kuɗi a hannunsu domin a dakatar da yaɗa hotunansu a intanet.
Mijin Fawzia yana sayar da ganye, kuma yana da yaran da ke aiki ƙarƙashinsa, sai dai wannan yanayin da ya shiga ya jefe shi cikin talaucin da ko madarar da jaririyarsu za ta sha ba ya iya saye.
Me ya sa Fawzia da mijinta har suka sayar da kayan amfanin su na gida domin kawai su biya bashi?
A cikin amsar wannan tambaya, akwai wani ɓoyayyen labari mai ban tsoro.
A shekara ta 2020, manhajar karɓar bashi cikin sauƙi ta fara aiki a Pakistan lokacin annobar korona.
A lokacin da masu karɓar bashin ke sauke manhajar suna ganin ƙa'idojin da aka gindaya kan duk wanda ya ci bashi, sai dai ba su yi tunanin hakan zai iya jefa su cikin masifa ba.
A misali, wa’adin biyan bashin shi ne kwana 91, kuma ana buƙatar biyan kuɗin ruwa kashi uku na kuɗin da aka karɓa.
Sai dai bayan mutum ya karɓi bashin a irin waɗannan manhajoji, bayan mako guda sai a fara buga masa waya da mabambantan lambobi, ana neman ya biya bashin, yayin da kuɗi a kullum suke hauhawa.
A duk lokacin da wani ya sauke wata manhaja daga kantin sauke manhaja na wayar Apple da wayar Android, ana nuna wata alama da ke neman izinin mai wayar don ba da dama ga manhajar ta riƙa samun duk bayanan da ke ƙunshe a wayar.
Da zarar mutum ya ce ya amince, shi ke nan kamfanin manhajar da aka sauke zai samu duk bayanan da ke cikin wayar mutum.

Asalin hoton, Getty Images
'Mijina ya yi yunƙurin kashe kansa sau biyu'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan shi ne abin da ya faru da Fawzia da mijinta.
An buga masa waya mako ɗaya bayan ya karɓi bashi, inda aka nemi ya biya kuɗin da ya karɓa, kuma ya haɗa kuɗin ruwa rupi 5,000.
Ta bayyana halin ƙuncin da ta shiga, 'Sun riƙa cewa mijina ya biya bashin ko kuma su yayata shi a cikin abokansa cewa ya ci bashi bai biya ba.
Mijina yakan ce musu ai wa'adin kwana 91 da aka bayar, ba su cika ba. Me ya sa suke matsa mana a kan sai mun biya bashin, haka dai muka samu da ƙyar muka biya rupi 5000.
Sai dai hakan bai tsaya a nan ba.
Ta ce "yanzu dai idan muka samu muka ci abinci sau ɗaya, sai mun jira an ba mu taimakon na gaba.
Ni da Mijina muna iya cin abinci, amma muna da jaririyar da ba ma iya saya mata madarar da take buƙata, kuma hakan ya sanya ta cikin wani hali."
Fawzia ta ce saboda halin da suke ciki na ƙunci, mijinta ya yi ƙoƙarin kashe kansa har sau biyu cikin ƴan kwanaki.
"Ya fitar da ni da 'yata daga cikin ɗaki, inda ya yi ƙoƙarin kashe kansa ta hanyar rataye kansa a jikin fankar sama. Sai kuma wata rana da ya gaji da kiran wayarsu, ya sake ƙoƙarin kashe kansa ta hanyar amfani da lantarki."
Mai yiwuwa ne akwai ɗumbin mutane irin Fawzia da mijinta, da suka faɗa cikin tarkon masu irin wannan manhajar ta bashi da ke fuskantar barazana.
Muhammad Masood mai shekaru 42 da ke Punjab na cikin waɗanda suka karɓi irin wannan bashi, kuma suke fuskantar barazana.
Ana zargin ya kashe kansa ne saboda irin wannan barazanar.
Bayan Muhammad Masood ya kashe kansa, mutane a shafukan sada zumunta sun riƙa kira a ɗauki matakin hukunta kamfanonin gudanar da manhajojin cin bashi.
Wane mataki aka ɗauka a kan masu ba da bashi ta intanet?

Asalin hoton, social media
Bayan zantawa da wasu daga cikin mutanen da suka faɗa cikin irin wannan tarko, BBC ta fahimci cewa da yawan mutanen sun kai ƙarar kamfanonin manhajar cin bashi, sai dai babu wani matakin a-zo-a-gani da aka ɗauka.
BBC ta tuntuɓi daraktan kula da aikata laifuka a intanet a birnin Islamabad, Ayaz Khan, domin sanin matakin da hukuma ke ɗauka a kan irin waɗannan kamfanoni da ake zargi da aikata laifukan cuta.
Ayaz Khan ya ce ya sha samun irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe da suka shafi manhajojin tsawon lokaci, kuma ya fara ɗaukar matakin bincike.
Ya ce " Mun tuntuɓi hukumar kula da kantunan sauke manhaja na Apple da Android sun kuma tabbatar mana cewa waɗannan manhajoji suna aiki ba tare da izini ba.
'Idan kuma an ba su izinin to suna karya dokar da ta tanadi kafa su".













