Sadiya Kabala: Masu karbar kayanmu bashi suna kokarin kassara mu
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
A baya-bayannan, kasuwanci shi ne babban abin da da dama daga matan Kannywood suke runguma a lokacin da suke cikin harkar fim din, ko kuma idan sun bar harkar fim.
A wannan hirar da BBC, daya daga matan na Kannywood wacce a yanzu ta ja baya da harkar fina-finan Sadiya Kabala ta ce neman makoma da neman tsira da mutunci ne ke sa matan rungumar kasuwanci.
Ta ce a baya matan Kannywood ba su fiya damuwa da neman wata sana'a ba bacin harkar fina-finai, abin da ya sa wasunsu ke shiga halin ka-ka ni-ka-yi idan sun bar harkar fim din.
To sai dai Sadiyan ta ce suna fuskantar babban kalubale inda masu karbar kayansu bashi suke kokarin kassara su.
