Yadda matsalar minshari ke shafar zamantakewar ma'aurata

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Suneth Perera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
"A baya ina wasa da iyalai da ƙawayena game da yadda mijina ke minshari sai dai a cikin zuciyata, abin na matuƙar damuna," in ji Arunika Selvam, wata matar aure mai shekara 45 daga Singapore.
"Ina damuwa cewa idan na yi magana da mijina a kan haka, ba zai ji daɗi ba."
Ta yi tunanin minsharin wani abu ne da ke zuwa da aure. Sai dai abin na yin mummunan tasiri a kan mijinta da kuma zamantakewarsu.
"Sai ya soma tashi sosai cikin dare sai kuma ransa ya riƙa ɓaci da safe," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
Minsharin da mijinta ke yi ya kuma hana ta samun yin bacci a tsanaki sannan kuma yanayin ya shafi aikinta saboda rashin isasshen bacci.
Abu ne na ruwan dare ka yi burus da abokin zama mai yawan minshari amma ƙwararru a ɓangaren lafiya da zamantakewa sun yi gargaɗin hakan na iya yin gagarumin tasiri kan lafiyar ma'auratan da kuma zamantakewarsu.
Mece ce matsalar barci mai alaƙa da numfashi ta 'sleep apnoea'?
Ana yawan alakanta minshari da matsalar bacci da a Ingilishi ake kira obstructive sleep apnoea (OSA), wani yanayi da numfashi kan tsaya sannan kuma ya dawo lokacin bacci, in ji ƙwararru.
Matsalar na sa gefe-gefen maƙogaro ya tsuke abin da ke hana numfashi da kyau sai kuma ya janyo raguwar yawan iskar da ke yawo cikin jini wato 'oxygen desaturation'.

A cewar Dakta Ramamurthy Sathyamurthy, wani likita kan numfashi da ke Jami'ar James Cook a Birtaniya, alamomin matsalar baccin ta sleep apnoea na iya bambanta, mara tsanani zuwa mai tsanani amma matsalar na iya taɓarɓarewa.
Ya yi gargaɗin rashin samun kulawa na iya shafar shi kansa mai minsharin da kuma lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwar abokin zamansu, har da sha'awa.
Mene ne alamomin matsalar barci ta sleep apnoea?
Alamomin galibi na faruwa ne idan mutum na bacci kuma sun haɗa da:
- Minshari mai ƙara
- Tsayawa da kuma fara numfashi
- Fitar da ƙara ta hanci
- Yawan tashi
Da rana kuma, masu fama da matsalar na iya:
- Samun ciwon kai idan sun tashi
- Yawan jin kasala
- Rashin samun nutsuwa
- Rashin yin tunani
- Damuwa da sauyawar yanayi
- Rashin tattara hankali wuri ɗaya
- Rashin sha'awa
Sauran matsalolin lafiya
Ƙari, matsalar barci ta sleep apnoea na iya haifar da wasu matsalolin lafiya.
Raguwar iskar da ke yawo a cikin jini da ke faruwa a lokacin matsalar na ƙara bugun jini, kamar yadda ƙwararru suka yi gargaɗi kuma hakan na iya ƙara haɗarin samun matsalolin lafiya da dama.
Wasu nazarce-nazarce da aka yi sun nuna matsalar ta OSA na iya ƙara haɗarin tsayawar bugun zuciya da kashi 140 cikin 100 da haɗarin shanyewar ɓarin jiki da kashi 60 cikin 100 sai haɗarin matsalar zuciya da kashi 30 cikin 100.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da wasu ma'aikata ka iya ganin minshari matsayin wani abin ban dariya, yana iya zama matsalar gaske ga zamantakewarsu, kamar yadda Dakta Sathyamurthy ya jaddada.
"Akasari, kashi 90 cikin 100 na marasa lafiyar da nake gani, suna zuwa ne saboda yana shafar abokin zamansu," ya shaida wa BBC.
Yana sa abokan zamansu su fara bacci a wasu ɗakunan, wani tsari na raba kwanciya.
Ba lalle bane ya zama mara kyau- wata mai bayar da shawara kan zamantakewa a Amurka, Sara Nasserzadeh tana yawan bai wa ma'aurata shawara su raba kwanciya ko da matsalar minshari ko babu. Soma rana da samun barci mai kyau na ƙara inganta zamantakewa, ta faɗa wa BBC duk da cewa wannan na iya faruwa ne kawai idan akwai wani ɗaki na daban.
Ga wasu ma'auratan, raba kwanciya na iya zama matakin farko ga rabuwar dindindin.
Tattauna matsalar
Duk da cewa Arunika Selvam tana zama a Singapore - ƙasar da ke da matuƙar ci gaba, tana da mafi arzikin ƙasa a duniya - samun wani gado daban a cikin gidan ba mai yiwuwa ne a wajenta ba.
"Dole sai da muka ba da hayar ɗakinmu na karɓar baƙi domin mu samu kuɗi saboda tsadar rayuwa a Singapore," in ji matar mai yaro ɗaya wadda ta shafe shekara 15 da aure.
Sai dai bayan jurewa rashin isasshen barci, Sevam ta yi wa mijinta magana game da matsalarsa ta minshari.
Bai yi yunƙurin zuwa wajen likita ba saboda mahaifinsa da kakansa suna minshari kuma yana ganin ba wani aibu a yinsa.
Ana yawan ganin minshari a maza a matsayin wani ɓangare na halayyar maza, musamman a tsakanin al'adun Asiya, in ji Selvam.

Asalin hoton, Getty Images
Sara Nasserzadeh ta ce a irin wannan yanayi, yana da muhimmanci a samu lokacin da ya dace a tayar da batun ta "lallami da hanya mai taushi".
"Wataƙila, bayan saduwa, wataƙila bayan shiga yanayi na jin daɗi," in ji Nasserzadeh, mawallafin littafin 'Love by Design - hanyoyi shida na gina rayuwar aure ta har abada.
Ƙwararren kan yadda tunanin wasu ke shafar jama'a ya ce yana da muhimmanci a tuna cewa mai minshari yana yawan jin kunyar matsalar.
Tasiri
A cewar ƙungiyar masu fama da minshari da matsalar bacrci ta Sleep Apnoea, akwai masu minshari miliyan 15 a Birtaniya kuma yana shafar mutum miliyan 30 a ƙasar - kusan rabin al'ummar ƙasar.
Kididdiga daga nazarin baya-bayan nan ta nuna adadin mazan da ke minshari ya fi mata, in ji ƙungiyar.
Sai dai koma wane ke minsharin, matsalar na iya yin mummunan tasiri.
Wasu rahotanni na nuna cewa yin minshari yana cikin galibin abubuwan da ke janyo rabuwar aure a Amurka da Birtaniya duk da cewa abu ne mai wahala ka samu takamaimen bayani da zai tabbatar da iƙirarin.

Asalin hoton, Getty Images
Rita Gupta, wata lauya daga Birtaniya, ta ce ofishinta ya samu ƙorafe-ƙorafe da suka shafi rabuwar aure sakamakon minshari.
"Tabbas rabuwar aure na yawan tasowa a matsayin dalilin rashin jin daɗi a auratayya," ta faɗa wa BBC.
"Ina samun mutane da dama da suke cewa 'muna kwana a ɗaki daban-daban na tsawon shekaru saboda yadda yake minshari kuma mun yi baya-baya da juna," ta ƙara cewa.
Lauyar ta ce wata matsala da aka fi kawowa a batun saki shi ne rashin mayar da hankali wajen samun magani da rashin ɗaukan matakan da suka kamata a bi wajen magance matsalar.
"Misali, ƙara ce kan wani mutum kuma matarsa tana cewa, "Yana yawan yin barci. Yana shafar barcina. Bai ɗauki wani mataki ba na magance matsalar."
Me ya kamata ka yi game da minshari ko 'sleep apnoea'?
Maganin matsalar barci ta 'sleep apnoea' na iya kawo sauyi a yanayin rayuwar mutum:
- Rage ƙiba
- Daina shan taba
- Taƙaita shan barasa
Sai dai ga galibin mutane, amfani da na'urar CPAP da ke taimakawa wajen buɗe hanyoyin numfashi na da muhimmanci.
Yana taimakawa wajen aika iska cikin takunkumin da mutum ke saka wa a kan bakinsa ko hanci lokacin barci.

Asalin hoton, Getty Images
Dr Ramamurthy Sathyamurthy ta ce yana da muhimmanci ka fifita lafiyar abokin zamanka da kuma mai minshari, ƙarfafa musu gwiwar zuwa neman shawarar likita.
"Zai amfanar ba wai kawai ga zamantakewa ba har ma ta fuskar kuɗi saboda mutane za su kashe kuɗi kaɗan wajen sayen magani saboda wasu matsalolin lafiyar da matsalar kan haifar. A don haka, yana zama alfanu ga iyalai baki ɗaya," ya ƙara da cewa.
Matsalolin kuɗi da al'ada
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Halayyar da ake nunawa kan minshari a duniya da kuma ɗaiɗaikun mutane, sakamakon batutuwan da suka shafi kuɗi, da zamantakewa da al'adu, da ma jinsi.
Saman (ba sunansa na gaskiya ba), wani mutum mai neman jinsi ɗan shekara 40 da ke aiki a matsayin mai kula da walwala a wani otal da ke Colombo . Suna ganin masoyinsa, abokinsa ne kawai da ke hayar wani ɗaki a gidansa.
"Abokin rayuwata yana da yawan minshari kuma bana iya barci saboda minsharinsa. Ina iya samun barci me daɗi ne kawai idan mahaifiyata ta ziyarce ni," in Saman da yake faɗa wa BBC.
"A wadannan ranakun, abokin zamana yana yi wa mahaifiyata tayin ta kwana a ɗaya ɗakin, yana sa ta yi tunanin ɗakinsa ne, yayin da yake barci a kan kujera," ya ce.
"Shi ne lokacin da kawai nake samu na samu bacci cikin natsuwa."
"Masoyina yana ganin kansa a matsayin mai halayyar mata, amma minshari abu ne da ake dangantawa ga maza a al'adarmu. Ina tsoron tattaunawa kan wannan batun na iya ɓata masa rai kuma yana iya sa ya rabu da ni," ya ƙara da cewa.
Yayin da Saman ya samu ƙwarin gwiwar tattauna matsalar minsharin da abokin zamansa, Selvam a ƙarshe ta shawo kan mijinta ya tuntuɓi wani likita, da ke sa a gano matsalar barci ta sleep apnoea.
Selvam ta ce mijinta tuni ya ɗauki mataki ta hanyar soma motsa jiki da nufin rage ƙiba.











