Pro League na son Lukaku, Everton ka iya rasa Calvert-Lewin

Mai kai hari na Belgium da taka leda a Chelsea Romelu Lukaku, mai shekara 31, ya bai wa Pro League na Saudiyya damar tattaunawa da shi, sai dai ya na nuna sha'awar AC Milan, da Napoli musamman son hadewa da tsohon manaja Jose Mourinho a Fenerbahce. (Telegraph, subscription required)

Duk wani yunkuri da Lukaku zai yi na komawa Napoli, zai tabbata ne idan sun yi nasarar sai da dan wasan Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25. (Times, subscription required)

Everton na cikin hatsarin rasa mai kai hari na Ingila Dominic Calvert-Lewin, inda za ta yi musayarsa a shekarar 2025, bayan samun tsaikon tattaunawa kan kwantiragin dan wasan mai shekara 27. (Football Insider)

Kungiyoyin Premier League shida wato Chelsea, Aston Villa, Newcastle, Everton, Nottingham Forest da Leicester na tsaka mai wuya wajen sayar da 'yan wasa kafin karshen watan nan domin raba ribar da suka samu. (Sky Sports)

Manchester United ta samu fam miliyan 60 a kan mai tsaron gida na Lille wato Leny Yoro, mai shekara 18, sai dai ta na fuskantar matsala kan sanya amincewar matashin dan wasan na Faransa da kungiyar Real Madrid. (Marca, in Spanish)

Chelsea na son dan wasan Faransa mai taka leda a Crystal Palace a ajin 'yan kasa da shekara 21, Michael Olise, 22, kuma ta na son dauko shi a kakar wasa mai zuwa. (Standard)

'Yar wasan gaba ta Sifaniya mai taka leda a Barcelona, Mariona Caldentey, mai shekara 28, ta amince ta shiga gasar Super League ta mata, idan kwantiragin ta da Arsenal ta kare a watan Yuni. (Sky Sports)

Borussia Dortmund na son dauko dan wasan baya na Dutch Ian Maatsen mai shekara 21, a zaman din-din-din, kan darajar fam miliyan 35. (ESPN)

Brighton na son dauko dan wasa Fabian Hurzeler mai shekara 31, a cikin jerin manajojinsu nan gaba. Kociyan haifaffen Amurka ya yi aiki da St Pauli domin samun ci gaba a kaka biyu a Bundesliga. (Telegraph, subscription required)

Brighton sun tattauna da tsohon manajanta Graham Potter, mai shekara 49, kan ko zai iya komawa kungiyar . (Guardian)