Mene ne ke janyo yawan son cin ƙwalama?

    • Marubuci, Onur Erem
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Alaƙarmu da abinci na da sarƙaƙiya, kuma a mafi yawan lokaci akwai illa.

Shin ka taɓa samun kanka kana ciye-ciyen kayan ƙwalama ko da bayan ka gama cin abinci? To kana iya faɗawa cikin rukunin ci-ma da ƙwararru suka bayyana a matsayin "hedonic eating" wato cin abinci don ƙwalama.

"Cin abu ba don yunwa ba amma saboda sha'awar cin abinci domin kwantar da ƙwalama," shi ne yadda masana kimiyya suka yi bayani, ɗabi'ar cin abinci da aka raɗawa suna "hedone," wata kalmar Girka da take nufin "sha'awa."

Duk da cewa akwai sha'awa a kusan duk abincin da ake ci, yawan son cin ƙwalama ba don samun kuzari ba, ana danganta shi da yankunan da ake sauƙin samun abinci kuma babu matsalar yunwa.

Mece ce yunwar kwantar da ƙwalama?

Jikinmu na samun karsashi daga kuzarin da ake samu daga abinci ko abin sha. Idan muka ƙona sinadaran ƙara kuzari fiye da wanda muke ci, to jikinmu yana mayar da martani ta hanyar ƙara sha'awar cin abinci. Wannan na faruwa saboda cikinmu yana da wani tsari da ke sanar da ƙwaƙwalwarmu idan babu abinci a ciki. Wannan ita ce yunwa kamar yadda kowa ya sani.

Yunwar ƙwalama na faruwa ne idan ba ma jin yunwa amma muna son cin abincu domin kwantar da ƙwalama, a cewar masana kimiyya.

"Kusan kowa yana da wannan ɗabi'ar kuma kowa yana da wasu ɗabi'u da sha'awa ke sa a yi su," in ji James Stubbs, Farfesa kan sha'awar cin abinci da daidaita kuzari a jami'ar Leeds da ke Birtaniya.

"Ga wasu, cin abinci sha'awa ce."

Farfesa Stubbs ya ƙara da cewa baya ga sha'awa, ɗabi'unmu na cin abinci galibi na da alaƙa da wasu abubuwan kamar yanayin mutum da kaucewa gajiya da rashin jin daɗi, wanda ya ce "ya sa ba a iya tantance bambancin yunwa da kwantar da ƙwalama.

Amma kwano ne cike da ganyayyaki ko yankakken kabeji da mutane ke ci idan suna jin sha'awar cin abinci.

"Muna jin daɗin samun abinci mai kitse da yawa da gishiri da sukari saboda hanyoyin samun kuzari ne," in ji Dakta Bethan Mead, malami kuma mai nazari a jami'ar Liverpool.

"Muna son irin waɗannan ci-maka saboda kuzarin da suke bamu da kuma ƙwalamar da suke kwantarwa idan ana cin su kuma yana da wahala a iya bambance tsakanin son cin abinci don kwantar da ƙwalama ko kuma cin abinci saboda yunwa."

Haɗarin yin matsananciyar ƙiba

Ana ganin ƙaruwar irin waɗancan abinci da ke da kitse mai yawa da gishiri da sukari a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ke sa cin abinci don kwantar da ƙwalama.

Kuma ana danganta yawan son cin kayan ƙwalama da matsananciyar ƙiba.

"A yanzu akwai kayan ƙwalama iri-iri zagaye da mu," in ji Farfesa Stubbs.

"Wannan na buɗe ƙofar yin ƙiba da matsananciyar ƙiba. Ba abin mamaki bane cewa ɗaya cikin mutum takwas a duniya a yanzu na fama da matsananciyar ƙiba."

Me za mu iya yi?

Ba lalle a ga illa a cin abinci don kwantar da ƙwalama ba, a cewar ƙwararru, saboda yana kwantar da kwaɗayi amma haɗarin cin abinci fiye da ƙima da yin ƙiba matsananciya abin damuwa ne.

Wani bincike daga Turkiyya da aka buga a Janairun 2024 a mujallar Human Nutrition and Dietetics ya yi nazari kan alaƙar da ke tsakanin yunwar kwantar da ƙwalama a tsakanin manya masu fama da matsananciyar ƙiba.

Sun gano cewa yayin da yunwar kwantar da ƙwalama ke ƙaruwa a tsakanin manya masu ƙibar da ta wuce ƙima, ƙwarin gwiwar da mutum ke da shi a karan kansa ta fusƙar ƙiba shi ma na ƙaruwa.

To me ya kamata mu yi domin kaucewa cin abinci fiye da ƙima sakamakon yawan son cin ƙwalama?

“Bincike ya nuna cewa yunwar son cin ƙwalama na iya raguwa idan mutane suka rage ƙiba," in ji Dr Mead.

"Tana iya yiwuwa mutanen da ke fama da wannan suna iya sauya alaƙarsu da nau'ikan abincin, ko ma yadda suke iya kwantar masu da ƙwalama ka iya sauyawa."

Rage ƙiba da rungumar sabon tsarin cin abinci, ba abu ne da zai zo da sauƙi ga mutane da dama ba. Amma akwai hanyar da za a iya juya hakan ya koma cin abu don kwantar da ƙwalama, in ji Farfesa Stubbs.

"Misali, idan kana son ƙara yadda kake motsa jiki, yi tunanin abubuwan da za ka ji daɗin yin su.

Masu bincike sun ce son cin kwalama zai ragu idan mutane suka rasa kiba'', in ji Dakta Mead.

“Watakila mutanen da ke cin wannan ka iya sauya yadda suke jin kwayin abinci.''

Rage ƙiba da ɓullo da sabuwar ɗabi'ar cin abinci, ko rungumar sabuwar rayuwar ba abu ne mai sauki ga mutane da dama ba. To sai dai akwai yadda za a sauya sha'awar son cin kayan kwalama, kamar yadda Farfesa Stubbs ya yi bayani.

“Misali, idan kana son ƙara yawan motsa jikinka, ka yi tunanin ɓullo da sabbin hanyoyin motsa jikin da kake sha'awarsu. Za a iya iya wurin motsa jiki? watakila ba haka ne. Zai iya zama yin tattaki da abokai ko rawa?

“Abu mafi muhimmnci shi ne ka gno wane abun da kake so ne ke ƙara maka ƙarfin gwiwwa don ka yi kokarin haɗa shi da ɗabi'arka da abubuwan da suka ba ka sha'awa.''

Kula da abin da kake ci ka iya zama hanyar da za ka rage wa kanka cin abinci mai yawa dangane da sha'awar abincin ƙwalama.

“Ba za mu iya hana mutane sha'awar abin ƙwalama ba'', in ji Farfesa Stubbs.

“Muna bukatar mayar da abin da yake ba mu sha'awar kn abubuwan da muke ci.”

Ya ce akwai yiwuwar gina sabuwar alaka d abincin da kake ci, ba tare da sun saɓa da abubuwan da akake sha'awa ba.

“Za ka iya tsayawa kan abin da muke kira tsarin rayuwa na 80:20,” in ji Farfesa Stubbs.

“Idan za ka ci kashi 80 na abinci maras ɗauke da sinadaran calorie, da ke cike da sinadaran da za su sa ka ji dadinsa, wanda hakan zai ba ka damar samu ragowar kaso 20 na sauran nau'ikan abincin.