Me ya sa wasu ƴan mata ba sa sanya hoton samarinsu a shafukan sada zumunta?

Hoton Tawana

Asalin hoton, Tawana Musvaburi

Bayanan hoto, Tawana
Lokacin karatu: Minti 5

Tawana Musvaburi tana da mabiya dubu 33 a shafinta na Instagram. Sannan mabiyan nan nata kusan sun san komai game da rayuwarta.

To amma yawancin mutane ba su da masaniya a kan wane ne saurayinta.

An ga wani hoto da ta sanya a shafin nata, tana tare da saurain nata suna shaye-shaye, har suna haɗa kofi.

Tawana, mai shekara 24, ba ta nuna hoton saurayin nata. "A matsayina na mace ina son in nuna cewakomai na ƙarƙashin ikona," in ji ta.

Wannan matashiya Tawana, mai tasiri a shafukan sada zumunta tana yawancin ayyuka da harkokinta ba tare da sanya saurayinta ba.

"Bai kamata mu ji kamar mun zama abin da muka zama ba ne na samun nasara a rayuwa, da taimakon namiji ba. Ina jin daɗi da farin ciki saboda na samu komai da nake so a rayuwa ta hanyar ƙwazona,'' kamar yadda ta yi bayani.

Duk da cewa sun yi aure da saurayin nata, ba ta son ta bayyana wannan alaƙa tata ta aure ko rayuwa da masoyin nata.

" Ba na rubutu a kan rayuwata ta soyayya a shafin sada zumunta, saboda kawai mun yi aure," ta ce.

Tawana na ɗaya daga cikin mata da yawa da ba sa son sanya hoton wanda suke soyayya da shi a shafin sada zumunta da muhawara.

Hoton Tawana na zaune tana shan wani abu a kofi da jarida a hannunta

Asalin hoton, Tawana Musvaburi

Bayanan hoto, Tawana
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata ɗaya da ya wuce mujallar Vogue ta wallafa rahoto a kan wannan batu.

Sunan maƙalar shi ne, 'Shin ya zama abin kunya ne a yi budurwa?', inda batun ya zama abin tattaunawa a shafin TikTok da Instagram.

Wadda ta rubuta maƙalar, Chante Joseph, ta ce matan da ke soyayya da maza ba kasafai suke magana a kan alaƙar ba a shafukan sada zumunat.

Duk da cewa za su iya cin moriyar soyayya da saurayin, to amma ba sa so a nuna cewa ba su da wani tunani a kan komai da ya wuce saurayi

Marubuciyar ta ce sanya hoton saurayi a shafin sada zumunta na zama wani abin kunya, kuma ana yi wa hakan kallon cewa abu ne na rashin kamala a zamanin yau.

Ta ce a yanzu ba a kallon samun saurayi a matsayin wani abin cigaba, hakan ba ya ƙara wa mace daraja kamar yadda ake kallon haka a da, a cewarta.

Chante ta bayyana cewa: ''Ɗaya daga cikin dalilan da ke sa mata ba sa sanya hotunan abokan soyayyarsu a shafukan sada zumunta, saboda su ƙalubalanci tsarin da maza ke yi wa mata danniya ne.''

Hoton Stephanie

Asalin hoton, Stephanie Yeboah

Bayanan hoto, Stephanie

"Mata da yawa na nuna cewa abu ne mai kyau a samu namijin da za a aura ko kuma miji . To amma a yanayin siyasar yanzu muna buƙatar mu tsaya mu natsu mu yi la'akari da alaƙarmu da maza," ta ce.

Stephanie Yaboha ta wallafa wani littafi mai suna 'South London'. Ita ma mai tasiri ce a shafin sada zumunta.

Ta yi nadamar sanya hoton saurayinta a shafin Instagram.

"Mutane da yawa sun daina bi na ta shafin saboda suna ganin idan kana da saurayi, abin da ka gani ba zai sake burge mu ba. A rana ɗaya mutum 1,000 suka daina bi na a Instagram," in ji ta.

Ta bayyana cewa masu alaƙa ko binka a shafukan sada zumunta ba sa jin daɗi su ji wani abu a kan saurayin da kike da shi.

"Babu wani abu na rashin dacewa ko rashin daɗi a kan magana game da soyayyarka. Mutane ba sa jin daɗin ganin hakan," in ji ta.

Hoton Dr. Gillian Brooks

Asalin hoton, Dr Gillian Brooks

Bayanan hoto, Dr. Gillian Brooks

Mai bincike a kan abubuwan da ake sanyawa a shafukan sada zumunta da kuma masu tasiri a shafukan Dr. Gillian Brookes, a King's College da ke London, ta ce masu tasiri a shafukan sada zumunta tuni sun riga sun sayar da kyawunsu."

"Akwai mutanen da ba abin da suke bi a kanka illa kamanninka ko hotonka saboda haka abu ne mai wahala ka zo musu da wani sabon kamanni ko hoto saɓanin wanda ka gabatar musu tun da farko," ta bayyana.

Ta ƙara da cewa: "Idan mai tasiri a shafin sada zumunta ba ya samun irin bayanin da yake tsammani, ba wanda zai bi shafinsa. Idan ba sa sanya hotuna ko bidiyo da sauran abubuwa da masu binsu suke so ba wanda zai bi shafinsu."

Masu tasiri a shafukan sada zumunta ba sa son a ɗauke su a matsayin waɗanda suka dogara ga samarinsu.

Ba a shafukan sada zumunta ba kaɗai, akwai tarin matan da ba sa so su fito fili su bayyana saurayin da suke soyayya da shi.

Hoton Dr. Gwendolen Sidman

Asalin hoton, Dr Gillian Brooks

Bayanan hoto, Dr. Gwendolen Sidman

Millie mai shekara 25, ta auri saurayinta da suka yi shekara biyar suna soyayya. To amma ko alama ba ta son sanya hotonsa a shafin sada zumunta tun ma kafin su yi aure.

"Ba na son kowa ya ɗauka cewa na dogara ne a kanshi. Rayuwata gabaɗaya ba ta dogara a kan alaƙarmu da shi ba," ta ce.

Ta ce kamannin da shafukan sada munuta suke ƙirƙira a kan mutum taƙaitacce ne.

"Idan aka sa hoton saurayina da na mu'amullarmu a shafin sada zumunta , hakan zai sa na ji cewa kamar ba ni da wani tunani da zan yi da ya wuce na soyayyar," in ji Millie.

Charlotte, mai sheakara 20, tana soyayya tsawon shekara biyu. Tana da dalilai masu yawa na ƙin sanya hotunan saurayinta a shafin sada zumunta.

"Ba mu da wani hoto da za mu sanya a Instagram. Bugu da ƙari ma soyayyata da shi, abu ne na sirri a tsakaninmu," kamar yadda ta bayyana dalilanta.

Arita, mai shekara 21, ta yarda da maganar Charlotte. Ta yi amanna cewa sanya hoton saurayinta a shafin sada zumunta, "zai sa aga kana da kyau."

"Ba na son mutane su gan shi su yi kishi. Za su iya yin kishi ba ma tare da sun sani ba, walau sun yi niyya ko ba su yi ba," in ji ta.

Dr. Gwendolen Sidman, ƙwararriya a kan halayyar mutane a jami'ar jihar Michigan da ke Amurka ta gudanar da bincike a kan soyayyar intanet.

Ta bayyana cewa mutane da yawa ba sa son sanya bayanai ko abubuwan da suka shafi rayuwarsu a shafukan sada zumunta, saboda suna ganin duk bayanin da aka sanya aintanet zaidade bai ɓace ba

"Yanzu mutane da yawa na rage bayanan da suke sanyawa a shafukan sada zumunta. Sun san cewa duk abin da suka sanya a intanet zai dawwama har abada. Ya da ce mutum ya yi hankali saboda ba za a iya goge bayanan ba," kamar yadda ta bayar da shawara.