Barcelona ta ɗauki Szczesny zuwa karshen kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ɗauki tsohon wanda ya tsare ragar Arsenal, Wojciech Szczesny zuwa karshen kakar nan, sama da wata ɗaya bayan da ya yi ritaya.
Tsohon golan tawagar Poland, mai shekara 34 ya sanar da yin ritaya ranar 27 ga watan Agusta, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Zai maye gurbin Marc-Andre ter Stegen wanda ya ji rauni a gwiwa a wasan La Liga da Barcelona ta doke Villareal 5-1 a cikin watan Satumba.
Szczesny ya tsare ragar Arsenal karo 181 tun bayan da ya koma Emirates yana da shekara 16, wanda ya yi gola a Brentford da Roma da kuma Juventus.
Ya koma Juventus A 2017, wanda ya tsare mata raga karo 252 a kaka bakwai da ya yi a birnin Turin da lashe Serie A karo uku da kuma Coppa Italia uku.
Wanda aka haifa a Warsaw ya buga wa Poland karawa 84, ya wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai sau hudu da zuwa gasar kofin duniya biyu.
Watakila Szczesny ya fara tsare ragar Barcelona a wasan La Liga da za ta kara da Deportivo Alaves ranar Lahadi.
Ranar Asabar, Osasuna ta doke Barcelona 4-2 ta kawo karshen wasa bakwai da ta lashe a jere da fara kakar bana.
Barcelona karkashin koci, Hansi Flick ta caskara Young Boys 5-0 a Champions League ranar Talata.











