Ko taron China da Afrika zai ƙara ƙarfin tasirinta a nahiyar?

Shugaba Xi a yayin bude taron Focac

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Xi Jinping ya yi alƙawalin dala biliyan 50 na zuba jari a Afrika
    • Marubuci, By Paul Melly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa analyst
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙara ƙarfi, shi ne China ke ƙoƙarin yi a sassan Afrika.

Yayin da tasirin wasu a nahiyar ke fuskantar barazana - misali Faransa da sauran ƙasashen Tarayyar Turai waɗanda hukumomin soji na Sahel suka juya wa baya, da kuma tayin sojojin haya na Rasha da wasu gwamnatocin Afrika aminan ƙasashen yammaci ba su yi amnna ba - China ta kasance ƴar ba ruwanmu.

Wakilai daga ƙasashe 50 na sassan Afrika sun amince su da gayyatar Beijing a taron China da Afrika a wannan makon.

Shugabannin ƙasashe da dama suka halarci taron - ciki har da António Guterres, shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya.

Cikinsu akwai shugaban Congo-Brazzaville Denis Sassou-Nguesso da kuma sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye - wanda aka ba sahun gaba kusa da shugaba Xi Jinping a hoto tsakanin shugabannin da suka halarci taron.

Ga gwamnatocin Afrika da ke fuskantar matsin lamba daga siyasar duniya kan fitowa su bayyana inda suka dogara, China yanzu za ta kasance babbar aminiya ba tare da tsangwama ba daga aminan Rasha da kuma ƙasashen da ke ƙawance da Turai da kuma Amurka.

Beijing na son ƙarfafa tattalin arzikinta da kuma neman albarkatun ƙasa, tare da tayin tallafin samar da ci gaba da kuma gina abubuwan more rayuwa a Afrika.

Ma'aikata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, China ta yi fice wajen gudanar da ayyukan ci gaba a Afrika

Ana zarginta da tursasa wa ƙasashen Afrika karɓar rance, kuma ta ƙi amincewa ta shiga ƙoƙarin ƙasashen duniya na yadda za a sassauta hanyoyin biyan bashin da ya yi wa wasu ƙasasshe katutu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ko yanzu ta ki amincewa ta yi lamuni ga biyan bashin.

Akwai koke cewa China ta fi so ta yi aiki da ƴan ƙasarta, maimakon horar da ƴan Afrika.

Amma ga yawancin gwamnatocin Afrika wannan suka ce kawai

Abin da ya fi jan hankalinsu yadda China ba ta damu da harakokinsu ba ko shiga lamurran siyasarsu.

Tabbas China ta ja hankali musamman ayyukanta a ɓangaren sufuri, ɓangaren da masu zuba jari na ƙasashen yammaci ke taka-tsantsan

Juyin mulkin 2023 a Nijar bai hana China kammala aikinta ba na shinfida bututun mai kilomita 2,000 zuwa Benin.

A Guinea, ƙarƙashin mulkin soja, kamfanin China ne ke aikin shinfiɗa layin dogo mai nisan kilomita 600, aikin da gwamnatocin Guinea suka daɗe suna neman taimakon ƙasashen duniya ba su samu ba.

Kuma a yayin taron Focac, China ta sanar da bayar da kuɗi sama da dala biliyan 50 na ci gaba da aikin

Amma a wannan karon akwai bambanci, domin taron ya fi mayar da hankali ne kan sabbin hanyoyin makamashi, ciki har da zuba jari a Afrika domin samar da motoci masu amfani da lantarki.

Wannan yana da muhimmanci musamman yadda yankin Asiya ya sha gaban nahiyar wajen bunƙasar manyan masana'antu.

Tutocin kasashe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tasirin China a Afrika ya sha bamban da sauran manyan ƙasashen duniya.

Haka kuma taron ya yi alƙawalin taimakawa wasu hanyoyi na samar da makamashi, inda shugaba Xi ya sanar da cewa China a shirye take ta samar da ayyuka 30 a ɓangaren makamashin nukiliya.

Wannan zai ja hankalin masharhanta na Afrika musamman yadda Faransa ta daɗe tana haƙo ma'adinin uranium a Nijar domin ɓangaren nukiliyarta amma ba tare da samar da ayyukan ci gaba ba a ƙasar da za a amfana shekaru da dama.

China ma na aikin haƙo ma'adinin uranium a Nijar

Sai dai Mr Xi ya yi ƙoƙarin kare China inda ya nuna tana cikin "ƙasashen kudancin duniya" tare da nuna cewa ƙasarsa da Afrika sun kai kashi ɗaya bisa uku na yawan al'ummar duniya.

Shugaban China da matarsa da kuma sauran shugabannin kasshen Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye kusa da shugaban China Xi Jinping a hoton shugabanni tare da matansu.

Taron ya amince da yarjejeniyar Beijing ta samar da "kyakkyawar makoma" da kuma muradun China daga 2025 zuwa 2027 na Beijing Action Plan

Ta buƙaci kamfanonin China su koma Afrika musamman yanzu da aka kawo ƙarshen barazanar annobar kora. Mista Xi ya bayyana manyan ayyuka, musamman samar da miliyoyin guraben ayyukan yi da kuma haɗin guiwa a ɓangarori da dama.

Sai dai babu cikakken bayani kan abin da yarjejeniyar China ta kuɗi yuan 360, wani mataki da ake gani na ƙarfafa tasirin kuɗin ƙasar.

Shugaban ya ce za a bayar da biliyan 210 na yuan kan bashi, yayin da biliyan 70 na yuan a ɓangaren zuba jari.

Ya kuma yi alƙawalin tallafin soji na dala miliyan 280 da kuma na tallafin abinci.

Yanzu ya rage a ga yadda za a raba tallafin, ko za a bi hanyoyin da za su kaucewa jefa wasu ƙasashen cikin ƙuncin bashi.

Masu rawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Taron Beijing ya fi mayar da hankali ne kan makomar tattalin arzikin Afrika

Yayin da bashi ya yi wa ƙasashe da dama katutu, musamman saboda tafiyar hawainiyar tattalin arziki da annobar korona ta haddasa, ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziki G20 ta samar da tsari na farfaɗo da ƙasashen.

China ba ta cikin shirin na ƙoƙarin saita ƙananan ƙasashe domin su biya bashin da ke wuyansu, inda masu suka ke zarginta ba ta yin abin da ya dace.

Amma a yanzu da ma shekaru masu zuwa, wannan taron na Focac alamu ne na iya samun sauyi.

Yayin da zuba jarin ƙasashen yammaci a Afrika, musamman na kudu da sahara, ya mayar da hankali kan ma'adinai da mai da gas da noma, Rasha kuma ta mayar da hankali kan tsaro, China kuma tattalin arziki.

Sai dai abin tambaya a nan ita ce, bayan kalaman Mista Xi, ko wannan zai iya zama dalilin karkatar da tattalin arzikin ga sabbin ɓangarori musamman makamashi?

Kawo yanzu dai babu tabbas kan ko dangantakar da ke tsakanin China da Afirka na shirin yin wani muhimmin sauyi.

Paul Melly mai sharhi ne kan manufofin Afrika a cibiyar Chattam House da ke London.