Majalisar dattijan Najeriya za ta iya adawa da bukatar CBN ta dala

Asalin hoton, Senate
Majalisar dattijan Najeriya ta yi maraba da ƙudurin da shugaban Babban Bakin ƙasar Olayemi Cardoso ya gabatar musu, na neman sanya dala biliyan 10 a kasuwar musar kudaden ketare ta ƙasar.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar ƙasar sun ce da za a karkata kudaden zuwa wajen samar da abinci da sai ya fi zama alheri ga al’umar Najeriya.
Cikin waɗanda suke da wannan ra'ayi akwai Sanata Babangida Husaini wanda ya fito daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.
Ya ce maimakon sanya waɗannan kuɗaɗe a kasuwar musayar kuɗaɗen ketare da take da buƙatar da ta fi haka, gwara a sanya su a harkokin noma.
"Mu abin da muka shaida wa Olayemi Cardoso shi ne, dala biliyan 10 ba za ta yi wani tasiri ba.

Asalin hoton, Senate
"Na ba shi misali da za a samu manoman shinkafa 30 ka ba su aron naira biliyan 10 da kuɗin ruwan da bai fi kashi bakwai ko takwas ba, ka basu hekta dubu goma ta shin kafa, ko wannesu zai iya noma maka shinkafa akalla ta tan dubu 100, idan aka casheta za ta iya kai tan miliyan biyu.
"Mu a wajen mu waɗannan muka fi damuwa da su, duk abin da aka faɗa idan dai mutanenmu ba za su samu wadatar kayan abinci ba to mu a wajenmu hankalinmu ba zai kwanta ba," in ji Sanatan.
Da yake bayani ga majalisar Shugaban babban bankin Olayemi Cardoso ya ce da suna gudanar da bincike sun gano cewa akwai kimanin kudaden ƙetare da ake bin su da yakai, biliyan biyu na dala, wanda suka gano na bogi ne shi ya sa har yanzu ba su biya su ba.
Wannan ya sa Sanata Osita B. Izunaso da ya fito daga jihar Imo ya nemi a toshe hanyoyin da dala ke zirarewa ba tare da hankalin gwamnatin ya je wurin ba.
Ya nemi a toshe hanyoyin samun dala irin na tallafin kudaden tafiya da ake bayarwa da na tallafin makaranta, yana cewa duk wanda zai iya kai yaransa makaranta waje to ba ya buƙatar sai gwamnati ta tallafa masa.
Wannan ya sa CBN ya yi alƙawarin sake duba hanyoyin da za a bi domin toshe duk wata kafa da dalar take zirarewa.
Sharhin masana
Masana tattalin arziki da bibiyar lamuran yau da kullum na da irin wannan ra'ayi da mafi yawan sanatocin Najeriyan ke da shi.
Aliyu Da'u Aliyu tsohon ma'aikacin banki ne, ya ce babu shakka idan aka sa wannan adadi na dala a kasuwa farashi da buƙatar da ake da su za su ragu da dama.
"Tabbas idan ka kawo dala biliyan 10 cikin kasuwa za a ji ta, za ta jijjiga kasuwa, har farashi zai iya sauka.
"Amma tambayar a nan ita ce, daga ina za a kawo dalar, domin ba mu da ita a Najeriya, sannan idan ta ƙare sai a yi yaya?, dole a bullo da shirye-shirye da za su iya ɗorewa.
"CBN da ma'aikatar kudi ya kamata su zauna su taimakawa jama'a ya zama irin wadannan abubuwan da muke shigo da su daga wajen ya zama muna iya samar da su a nan Najeriya," in ji masanin tattalin arziƙi Aliyu Da'u Aliyu.











