Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙabilun Afirka da ake gane su da billensu
Bille ko zane na cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su wajen gane ƙabila ko al'umma musamman a zamanin baya. A nahiyar Afirka, zane wata al'ada ce daɗaɗɗiya mai cike da tarihi, inda ake zana wa yara bille na al'adarsu tun suna ƙananan yara.
Sai dai yanzu al'adar na neman fara ɓacewa, inda yanzu matasa da dama suke ƙin zana wa ƴaƴansu da suka haifa, suna masu bayyana cewa yanzu zamani ya canja kuma an samu cigaba.
Wasu na yin zanen ne a kumatu, wasu a fuska wasu kuma a goshi, sannan akwai masu yi a jiki, kuma yawanci ana yi ne domin bayyana al'adu ko tambarin ƙabilar mutane, sannan akwai waɗannan suka yi amannar zanen na ba su kariya.
Akwai imani da al'umomin Yarbawa da Igbo suka yi cewa wasu yaransu da suka haifa suna mutuwa, sannan suna dawowa ta hanyar sake haihuwarsu saboda suna da alaƙa da wasu aljanu.
Shi ya sa ƙabilar Yarbawa ke billen Abiku ko kuma Igbo da ake kira Ogbanje saboda imani da suka yi cewa waɗannan yaran, na cikin ƴaƴan wasu aljanu da ke zaune a cikin manyan bishiyoyin Iriko ko kuka.
Shi ya sa suke musu zane domin ko da ƴan'uwansu aljanu sun zo ɗaukarsu, ba za su gane su ba.
A shekarar 2017 ce Sanata Dino Melaye ya gabatar da ƙuduri domin haramta bille ko zane a majalisar dattawa ta Najeriya
A lokacin, sanatan ya ce bai kamata a ci gaba da zanawa wa yara bille ba, ko da kuwa an yi su a baya saboda wasu abubuwa da suka danganci al'ada da tarihi.
Ga wasu manyan ƙabilun da zane ko bille ke da muhimmanci a al'adarsu:
Igbo
Ƙabilar Igbo na cikin manyan yarukan Najeriya guda uku, kuma ƙabilar na da mutane da dama da suka barbazu a Afirka, musamman a yankin Afirka ta Yammacin nahiyar.
Sai dai sun fi yawa a gabashin Najeriya, amma akwai su a ƙasashen waje kamar Amurka da Birtaniya da sauran ƙasashen duniya.
Daga cikin billen ƙabilar Igbo akwai Nsibidi da Ichi da Egbugbu da Uri (Uli) da Nki da Ogbanje.
Ƙabilar sun matuƙar aminta da zanen bille, inda wasu suke alaƙanta hakan da ba su kariya daga cutarwar aljanu da wasu camfe-camfen.
Hausa
Hausa harshe ne da ke da ɗimbin mutane masu amfani da shi a arewacin Najeriya da Nijar da ma wasu ƙasashen waje, ciki har da Saudiyya da Habasha da sauransu.
Hausawa na da zane kala-kala da ake yi wa yara tun suna jarirai domin nuna asalinsu da ma yankin da suka fito a cikin yankin na Hausawa ko kuma al'adarsu ko sana'ar da suka gada.
Daga cikin fitattun zanen Hausawa akwai kalangu na Katsinawa da zanen uku-uku na Kanawa da zanen Gobirawa -wanda shi ma akwai na'uka - da billen goshi da sauran zane daban-daban da ake yi a ƙasar ta Hausa a kumatu da goshi.
Yawanci wanzamai ne suke tsaga domin fitar da bille ga jarirai tun suna ƙananan yara, kuma wanzaman suna da tarihin alaƙa da irin billen da suka fi ƙwarewa.
Yarbawa
Ƙabilar Yarbawa ita ma tana cikin manyan ƙabilun Najeriya da suka yi fice wajen yi zane a fuska da goshi.
Zane na cikin al'adun Yarbawa da suke riƙo da su sosai, duk da cewa a yanzu ya fara ɓacewa a tsakanin matasan ƴan ƙabilar, musamman waɗanda suka taso a arewacin Najeriya.
Daga cikin fitattun zanen Yarbawa akwai uku-uku da suke kira Pele da ya fi yawa a tsakanin mutanen da Ile-Ife da Owu mai shida-shida da ya fi yawa a tsakanin mutanen Abeokuta da Gombo da ake kira da Keke da ya fi yawa a Ogbomosho da Abaja da ake yi a Oyo.
Sai kuma ƙananan billen Yarbawa irin su Ture da Mande da Bamu da Jamgbadi.
Nufawa
Nufawa wasu al'umma da suka yi yawa a jihohi arewa ta tsakiyar Najeriya, musamman jihohin Kwara da Neja da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Billen Nufawa da aka fi sani shi ne billen Kpelle wanda yake da matuƙar tarihin a tsakanin Nufawa, kuma yake da tasiri a al'adarsu.
Dagomba
Ƙabilar Dagomba ko kuma Dagbamba wasu al'umma ce da ke amfani da harshen Dagbanli, kuma al'ummar da ke amfani da harshen sun fi yawa a arewacin ƙasar Ghana.
Ana kiran zanensu da Dagomba Sigiligu, inda ake zane ƴan biyu a jikin kumatu a ranar sa suna.
Wolof
Wolof wata ƙabila ce da ta yi fice a tsakanin yammacin Senegal da arewa maso yammacin Gambia zuwa yankin Mauritania.
A ƙasar Senegal, ƙabilar Wolof ce ta fi yawan al'umma. Ana kiran su ƙabilar Wolof, kuma suna amfanin da harshen Wolf ne.
Mutanen Wolof suna da bille a goshi da zane a kumatu.
Kanuri
Ƙabilar Kanuri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun yi fice da yanayin zanensu na fuska.
Akwai zana daban-daban da ke nuna bambancin zuriya ko dangi daga cikin ƙabilar ta Kanuri, amma yawanci duk a fuska ne.
Akwai zuriya da dama a Kanuri kamar Wuje da Gumati da Manga da Bodoni da Kanembu da sauransu, kuma zanensu yana bambanta ne kaɗan.
Amma akwai billen Susa'na mai kwale huɗu=huɗu a sai bille ɗaya a goshi wasto zane tara.
Fulani
Fulani al'umma ce da suka fi yawa a ƙasashen Najeriya da Senegal da Mali da Guinea da Burkina Faso da sauran su.
Yawanci suna zane ne a kumatu da goshi, kuma zanen suna bambanta da yanayin harshe da ma dangi ko zurriya.
Mandinka
Mandinka ƙabila ce da al'ummarta suka fi yawa a kudancin ƙasar Mali da kudancin Senegal da gabashin Guinea.
Suna magana ne da harshen Mande, kuma suna cikin al'umma da suka yi yawa a nahiyar Afirka.
Suna yin zanen bille ne manyan-manya a goshi.