Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Daga bakonmu na mako: Barebari da al'adunsu na aure
Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan ƙabilun Arewacin Najeriya, waɗanda suka taɓa kafa ɗaya daga cikin dauloli guda biyu mafiya girma a duk faɗin Afirka ta yau.
Mutane ne da suka samo asali daga Yemen. Suna da matuƙar riƙo da al'adunsu na gargajiya, addini, karɓar baƙi da kuma uwa-uba hidimtawa Alƙur'ani da masu hulɗa da shi da suka shafi koyo, koyarwa, hadda, rubutawa da kuma masu karanta shi.
Babban garinsu; wato Maiduguri, ana yi masa kallon matsugunni ko kuma masaukin mahaddata da kuma makaranta Alƙur'ani.
Al'adunsu na aure
Haƙiƙa Kanurai suna ɗaya daga cikin ƙabilun da suka fi kowace ƙabila iya riƙon aure da gudanar da al'adu a yayin aure. Al'adun nasu sun haɗa da:
- Bawaram
- Fafurai
- Wushe - wushe
- Klatul
- Kalawa
- Ka'aji
- Humram
- Kulaicam
- Kalam - wuri
- Kndai
- Kususuram
- Wushe - wushen yaa'ye
- Nalle
- Tulur
- Ksai lewa
- Kaulu
- Ganga - kura
Bawaram: Kalmar Bawaram tana nufin babanni. Idan kuwa a aure ne aka ce Bawaram, to ana nufin kayayyakin da ango yake yi wa dangin amarya, waɗanda suka haɗa da:
- Ya - Uwa
- Kamu ba'aye - matar uba ko kuma matan uba
- Bawa - ƙannen uba da yayunsa
- Yakura - babbar yayar amarya
- Am ngawoye - mutanen baya
- Duhuram - mai kitso
- Ka'aram - kakanni
- Ya njimma - uwar ɗaki
Fafurai: Wani akwati ne da gidan amarya suke yi wa ango. Abubuwan da ake sakawa a cikin akwatin sun haɗa da, shaddodi da yadudduka da huluna da sallaya da turare da agogo da takalmi da sauransu.
Wushe - wushe: Biki ne da ake gudanarwa tsakanin ɓangaren amarya da na ango ana gobe ɗaurin aure. Ɓangarorin biyu su kan yi shigar al'ada irin ta Kanurai su haƊu a wata farfajiya ko kuma su kama fili domin yin wannan bikin.
A wajen bikin, ana keɓe amarya da ango akan ƙayatacciyar kujera, yayin da makaɗan gargajiya ke kiɗa, 'yan mata da samari suke rausayawa irin ta al'ada a gaban ango da amarya.
Daga nan kuma sai a shiga yi wa ango da amarya kari tare da ɗaukar hotuna. Wushe - wushe yana ɗaya daga cikin al'adar Kanurai wanda ƙabilu da dama suka ara suke gudanarwa yau a Najeriya.
Qlatul: - Yana nufin wanke kai, mata kaɗai ake yi wa. Ana yinsa ne idan aure ya saura kwana uku.
Yadda ake yin shi ne, babannin amarya ne suke wanke kan amarya da ruwan karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kiɗan ƙwarya; wanda tsofaffin mata suke waƙa cikin harshen Kanuri.
Shi wannan kiɗan ƙwaryar, ana yin sa tamkar irin wanda aka san Hausawa ne da shi.
Kalawa: Tamkar shaɗi yake, sai dai shi ba bugu ake yi ba.
Yadda ake yin sa shi ne, ana tanadar akushi da busasshen karkashi da farar shinfiɗa, sai a zo da ango ko amarya a ɗora a kan wannan shinfiɗar, daman an ɗora tuwon buski ko shinkafa akan wuta.
Ana sauƙewa za a ɗebo shi da zafinsa, sai ango ko amarya su buɗe tafin hannunsu, a zuba musu akai da zafinsa, sai su kuma (amarya ko angon) su juye abincin da aka zuba musu a tafin hannu a cikin wannan akushin.
Ana yin haka har sau uku, sannan sai a goge musu hannayensu, a shafa musu busasshen karkashin.
Daga nan sai 'yan uwa da abokan arziki su zo su yi musu kyaututtukan alfarma. Idan da wanda zai yi kyautar gida ko mota ko kuma jari, to a wannan wajen zai yi.
Ma'anar yin wannan al'adar shi ne, yadda suka riƙe wannan abincin da zafinsa, Allah ya sa su riƙe wannan auren fiye da haka.
Kalaji: Yana nufin turaren wuta. Ango ne yake bayar da kuɗin sayen turaren wuta wanda amarya take zuwa da shi ɗakinta. Wannan ma yana ɗaya daga cikin al'adar Kanuri wanda sauran ƙabilu suka ara a yau.
Humram: Wani turare ne na ruwa wanda mata suke shafawa a jikinsu. Shi ma ango ne yake bayar da kuɗin sayensa.
Kulaicam: Shi ma nau'in humram ne, sai dai shi da man shafawa ake haɗawa, a shafe jiki. Shi ma ango ne yake bayar da kuɗin sayensa.
Kalam - wuri: Wuri kuɗi ne na da da ake amfani da shi. Kalam - wuri wani abu ne ƙarami kamar kafbasa, wanda ake manne shi da kuɗi gaba ɗayansa a bai wa amarya ta tafi da shi ɗakin mijinta a matsayin kyauta.
Duk lokacin da buƙatar kuɗi ya sameta kuma babu kuɗi a hannunta, sai ta ɗaye wannan kuɗin da ke liƙe, ta yi uzurinta da shi.
Ita wannan al'adar, takwarar amarya ce take yi, idan kuwa ba ta nan (ta mutu), sai 'ya'yanta ko 'yan uwanta su yi.
Kndal: Kalmar Kndal asalinta Kanuri ce. Kndai wani ɗan kwano ne ko kuma akushi da ake saƙa shi da kaba (da Hausa sunansa Adudu).
Ana yi masa ado, sai a zuba goro da fure ko dabino a ciki amarya ita take zuwa da shi gidanta.
Idan mijin mai cin goro ne, sai ya yi amfani da shi; idan kuwa ba ya ci, ita ma ba ta ci; sai ta dinga sa dabino ko wani abu da take buƙatar ajiyewa a ciki.
Kususuram: Abin da ake nufi da Kususuram shi ne, kai kayan lefe. Yadda ake kai kayan lefe a al'adar Kanurai ya bambanta da na sauran ƙabilu.
Idan an tashi kai kayan lefe gidan iyayen amarya a al'adar Kanuri, ana haɗawa da tinkiya ko bijimi ko saniya.
Za a ɗaura atamfa a wuyan tinkiyar ko bijimin ko saniyar a yayin da za a kai kayan lefen.
Wannan atamfar da aka ɗaura a wuyan dabbar, idan an je gidan iyayyen amarya, suna ba da ita kyauta ga wanda ko waɗanda suka riƙe dabbar a yayin kai kayan lefen.
Wushe - wushen yaa'ye: Ana yinsa ne a ranar Alhamis. Yadda ake yi shi ne: dangin amarya ne za su haɗu su yi nakiya, a yayin da ɓangaren ango kuma za su kawo musu goro tare da yi musu sannu da aiki; sai ɓangaren amarya su ba su wannan nakiyar da suka yi.
Nalle: Yana nufin lalle ko sa lalle, ana yin sa a ranar Talata. Ɓangaren ango za su kai buhun lalle da cingam da minti har ma da goro da dai sauransu zuwa gidan iyayen amarya.
Tulur: Kalmar Tulur a Kanuri yana nufin bakwai. Shi Tulur a auren Kanurai kuma, yana nufin zaman bakwai da mace ɗaya ko biyu suke yi a gidan amarya na tsawon kwanaki bakwai.
A wannan zaman, waɗannan matan su za su riƙa yi wa amarya girki da shara da wanke-wanke da dai sauran hidindimun cikin gida har na tsawon wannan kwanaki.
Bayan kwanakin sun cika, ango yana yi wa waɗannan matan kyautar atamfa da sabulai da turare, wani ma har da 'yan kuɗaɗe.
Ksai lewa: Gaisuwar iyaye. Ana yinsa ne a washegarin ɗaurin aure, inda ango da abokanansa za su kai ziyarar gaisuwa zuwa wajen iyayen amarya.
Kaulu: Ango kaɗai ake yi wa; yadda ake yi shi ne, ana dama karkashi ne da ruwa, sai mahaifin ango, ko ƙanin mahaifinsa, kai wani lokacin ma maigidansa na wajen aiki ko sana'a ne zai shafe masa hannunsa da wannan ruwan karkashin.
Wannan fata ne na duk abin da ya mallaka ya yauƙaƙa (wato ya yi albarka).
Ganga - kura: Kiɗan gargajiya ne da ake yinsa ranar ɗaurin aure. Dangin amarya ne da na ango maza da mata za su haɗu su yi shiga irin ta al'ada su fito su rausaya a tsakanin juna.
Wasu labaran masu alaƙa
Jigon juriyar Kanurai
Waɗannan al'adun suna daga cikin jigon da ya sa Kanurai suka fi ƙabilu da dama juriya wajen riƙon aure.
Sai dai kuma a wani ɓangaren, wasu na ganin waɗannan al'adun suna daga cikin abin da ya sa auren Kanurai yake da tsada, duk da cewa ba dukkan Kanurai ba ne suke gudanar da waɗannan al'adun ba a yau, saboda yanayin da ake ciki.
Da wannan muka zo ƙarshen wannan maƙalar tamu a kan Kanurai da al'adunsu na aure.
Akwai bayani iya bakin gwargwadona game da tarihin ƙasar Barno da suna da asali da kuma wasu daga cikin kyawawan halayen Kanuri da abin da ya shafe su a littafin "ƘASAR BARNO A JIYA."
Daga Mohammed Bala Garba, Maiduguri. Za a iya samunsa a waɗannan lambobin: 08098331260 da kuma 08025552507.