Daga baƙonmu na mako: Kun san mawallafin fitaccen littafin Al-Arabiyyatul Jadeeda na Bari wa Biba?

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Mohammed Bala Garba, Maiduguri.Dukkan abubuwan da ke cikinta, ra'ayinsa ne ba na BBC ba.

Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya (wanda aka fi sani da Bari-Biba), littafin lugga ne da ya shahara a Najeriya har ma da wajenta.

Abu ne mai matuƙar wuya, mutum ya tashi a Najeriya (musamman a Arewa) kuma ya yi karatun addini musamman a Islamiyoyi amma bai san wannan littafi ba.

Mutane da dama ba su san wane ne mawallafin wannan littafin ba, illa dai sunansa da wasu 'yan tsiraru suka sani.

Hatta a shafukan sada zumunta na soshiyal midiya, hankalin jama'a ba ya kai wa ga tambayar wane ne wannan babban gwarzon da ya hidimtawa addini Musulunci ta hanyar rubuta wannan littafin.

Sai dai kawai wasu 'yan tsiraru da suke sanya hoton littafin da cewa, "Ko Bari da Biba sun yi aure zuwa yanzu?"

Duk da cewa a bangon littafin babu sunan mawallafin, amma a shafin farko na cikin littafin an sanya sunansa.

Wanda kuma hakan bai ja hankalin ɗaliban ilimi wajen tambayar bincikar tarihinsa ba.

Yau kimanin sama da shekaru Arba'in da samuwar wannan littafin (domin an fara buga shi a 1979), yau cikin yardar Ubangiji zan yi wa 'yan uwana almajiran ilimi da ma sauran al'umma ɗan takaitacce bayani game da tarihin mawallafin wannan littafi mai albarka.

Wane ne mawallafin Bari-Biba?

Wanda ya wallafa wannan littafi na Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya, shi ne, Sarkin Kazaure, mai martaba marigayi Alhaji Hussaini Adamu (mahaifin Sarkin Kazaure na yanzu).

An haife shi a garin Roni da ke gundumar masarautar Kazaure (ba mu samu sahihin shekarar da aka haife shi ba).

Ya yi karatun Firamare a Elementary ta Kazaure, daga nan ya tafi Middle da ke Kano. Bayan nan, ya halarci makarantar nazarin harshen Larabci, wato School of Arabic studies (S.A.S) da ke nan Kano.

Daga nan ya tafi Ingila don ƙaro karatu da yin nazari a jami'ar London. Bayan ya dawo gida Najeriya ya fara aiki cikin jihar Arewa a matsayin jami'i mai kula da fannin ilimi, daga bisani kuma ya koma koyarwa a makarantar (S.A.S).

Ya riƙe muƙamin mai kula da makarantun Firamare da Kwalejojin ilimi na Arewa a 1963 zuwa 1968. Bayan littafin Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya, Sarki Hussaini ya rubuta wasu litattafai kamar su:

  • Jagoran Musulunci
  • Fassarar littafin ibada da hukunce-hukunce (Daga harshen Hausa zuwa Larabci).

Sarki Hussaini yana ɗaya daga cikin mafi soyuwar sarakunan da suka mulki masarautar Kazaure. Ya kasance sananne malamin addini da kuma mai ƙwarewa musamman a ɓangaren Fiqhu da lugga.

Bayan haka, shi shugaba ne a fanni ilimi da raya karkara da wanzar da zaman lafiya da ayyukan addini.

Yana ɗaya daga cikin manyan marubuta waɗanda suka yi zamani da su Isa Kaita da Sa'adu Zungur da Abubakar Imam da dai sauransu. Maluntarsa ta yi gagarumar taimakawa wajen ci gaban addinin musulunci da ilimin zamani a ƙasar Hausa.

Shi ne sarki na tara a jinsin Fulani cikin sarakunan da suka mulki Kazaure. Kamar yadda ya zo cikin jadawalin sarakunan Kazaure. Ga su kamar haka:

  • Ibrahim Ɗantunku. Shi ne sarki na farko a jinsin Fulani. Ya yi sarauta daga shekarar 1819 zuwa 1824.
  • Dambo Ɗan Ɗantunku. Ya hau karagar mulki a 1824, an kashe shi a 1857.
  • Muhamman Zangi Ɗan Dambo. Ya hau sarauta a 1857, ya rasu 1886.
  • Muhamman Mayaƙi Ɗan Dambo. Ya hau karagar sarauta a 1886, ya ajiye sarautar saboda tsufa a 1914.
  • Muhammadu Tura Ɗan Muhamman Mayaƙi. Ya hau karagar sarauta a 1914, ya rasu 1922.
  • Ummaru Na'uka Ɗan Muhammadu Tura. Ya ci sarauta a 1922, ya rasu 1941.
  • Adamu Ɗan Abd Al-Mumini. Ya hau karagar sarauta a 1941, ya rasu 1968.
  • Ibrahim Ɗan Adamu. Ya hau karagar sarauta a 1968, ya rasu 1994.
  • Hussaini Adamu (mawallafin Bari-Biba). Ya hau sarauta a 1994, ya rasu 1998.
  • Najib Hussaini Adamu (sarkin Kazaure na yanzu). Ya hau karagar sarauta a 1998 bayan rasuwar mahaifinsa, kuma shi ne sarkin Kazaure har zuwa yau.

Marigayi Alhaji Hussaini yana daga cikin waɗanda suka samar da Jama'atul Nasril Islam. Hakan yana bayyana mana abubuwa da dama game da martabarsa cikin jerin khalifofin Sakkwato.

Shi shugaba ne da sunansa ya zama abin martabawa sakamakon ƙwazonsa da kuma kasancewarsa gagara misali a cikin al'umma.

Ya rubuta littafin Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya ne domin ƙarfafawa al'ummar Arewa gwiwa (musamman matasa da yara ƙanana) wajen koyon harshen Larabci a sauƙaƙe.

Ya rubuta littafin a lokacin yana matashi. Ya mulki masarautar Kazaure tsawon shekara huɗu (daga 1994 zuwa 1998).

Ya rasu a daren Asabar da misalin ƙarfe biyu cikin watan Oktoban 1998. Ya bar mata uku, da 'ya'ya goma sha shida da jikoki ashirin da biyar (a lokacin).

Daga cikin shahararrun 'ya'yansa akwai Sarkin Kazaure na yanzu, Mai martaba Alhaji Najib Hussaini Adamu, da Hajiya Rabi Hussaini Adamu Ishaq (tsohuwar kwamishiniyar ilimi ta jihar Jigawa)

Akwai kuma Dokta Hassana Hussaini Adamu (tsohuwar kwamishiniyar muhalli) da Hajiya Amina Bala Zakari (tsohuwar shugabar riƙon ƙwarya a hukumar zaɓe ta ƙasa) da ministan albarkatun ruwa Suleman Hussaini Adamu.

Haƙiƙa Sarki Hussaini ya yi matuqar ƙoƙarin da za a daɗe ana tunawa da shi bisa gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa gwiwar al'ummar ƙasar Hausa a fannoni da dama.

Wannan ta sa a 1998 aka sauyawa kwalejin kimiyya da fasaha ta Kazaure suna i zuwa Hussanin Adamu Federal Polytechnic Kazaure.

Muna addu'ar Ubangiji Allah Ya saka masa da mafifincin alheri, Ya gafarta masa, shi da duk waɗanda suka taimaka wajen yaɗa wannan littafin, Ya albarkaci bayansu, Ya ƙara ƙarfafa gwiwar masu irin tunaninsa a Arewa, Amin.