Tsagun fuska a Najeriya: Mutane na ƙarshe da suka rage da bille

    • Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Kwale, ko bille, abu ne da ya shahara matuƙa a Najeriya lokutan baya.

Yawanci ana yinsa ne ga mutane tun suna yara a dukkan kumatu biyu, ko tsakiyar goshi domin shaida su.

Zanen da ake yi a fuska na ƙunshe da labaran tsananin zafi, da kuma ƙara kyau.

Sai dai al'adar ta riƙa shuɗewa tun shekara 2003, lokacin da aka rattaba hannu kan wata doka da ta hana dukkan wasu abubuwa da ake kallo a matsayin ƙuntata wa yara.

Manyan da suke da bille a yanzu, su ne mutane na ƙarshe da ke ɗauke da alamar, kuma suna ta'allaƙa da yaruka da dama na Najeriya.

Zane-zane goma sha biyar da ke fuskar Inaolaji Akeem sun bayyana shi a matsayin wani dan masarautar Owu da ke jihar Ogun ta kudu maso yammacin Najeriya.

Malam Akeem haifaffen gidan sarauta ne, don haka akwai dogayen billaye a fuskarsa.

"Kamar rigar kwallon kafa ce," in ji shi, ya kara da cewa sun sanya shi shahara ƙwarai.

A wani muhimmin al'amari, Mista Akeem ya ce yana kallon zanen a matsayin muhimmin abu, kuma bai yarda cewa ya kamata ace mutane su riƙa yin shi kawai don ado ba.

Haka nan kuma bukatar yin bille ko tsagu a fuska ta yi karfi a arewacin Najeriya, musamman a tsakanin al'ummar Gobir na jihar Sokoto.

Kakannin Ibrahim Makkuwana, makiyaya da suka fito daga Gubur wato Sokoto a yau, ba su da alamar fuska. Amma, in ji shi, yayin da suke yawo don neman filayen noma, "sun yi yaƙe-yaƙe da yawa kuma sun ci wurare da yawa".

Daga nan sai suka yanke shawarar yin wata alama ta musamman a kuncinsu, "kamar irin wadda dabbobinsu suke da su, da za ta taimaka musu wajen gano 'yan uwansu a lokacin fadace-fadace", in ji Makkuwana.

Ya shaida wa BBC cewa "Abin da muka samu kenan."

Amma kuma akwai banbanci tsakanin Gobirawa.

Sai kuma 'ya'yan mahauta, masu billaye guda tara a gefe guda 11, a daya bangaren kuma masu biyar da shida a kowane bangare na nufin sun fito ne daga zuriyar mafarauta.

Game da masunta, suna da alamomi daban-daban da aka zana har zuwa kunnuwansu.

A halin da ake ciki kuma, a tsakanin Yarabawa da Igbo na kudancin Najeriya, wasu alamomi na da alaka da rayuwa da mutuwa.

Akwai imani da al'umominsu suka yi cewa an ƙaddara wasu yara su mutu kafin balaga.

An yi imanin cewa waɗannan yaran, Yarbawa, na cikin 'ya'yan wasu aljanu da ke zaune a cikin manyan bishiyoyin Iriko.

Abu ne da ya zama ruwan dare, mata kan rasa 'ya'ya da dama tun suna kanana a jere, kuma ana zaton yaron daya ne, amma suke sake fitowa suna azabtar da mahaifiyarsu.

Irin waɗannan yaran ana yi musu alama ko zane don kada a rika gane su.

A yanzu an fahimci cewa yawancin irin wadannan yara na mutuwa ne saboda cutar sikila

An yi wa Yakub Lawal da ke Ibadan a kudu maso yammacin jihar Oyo irin wannan zane na su wadannan yara da ake kiransu Abiku.

"Wannan ba shine zuwa na duniya na farko ba, na sha zuwa a baya ma'' in ji shi.

"Na mutu sau uku, kuma a dawowata ta huɗu ne aka min wannan tsagu'' in ji shi.

Abubuwan da ke da alaƙa da labaran yaran Abiku su ne waɗanda alamunsu ke tunawa da wani da ya rasu ko kuma wanda aka "sake haifuwa".

Shi kuwa Olawale Fatunbi wanda ke da tsagu hudu a tsaye da uku a kwance kakarsa ce ta yi masa.

Sai dai ya ce ba so hakan ta kasance ba.

"Ba na son su da gaske saboda ina ganin hakan a matsayin cin zarafin yara amma al'adarmu ce," in ji shi.

Da tsagu 16 a fuskarta dakyar a iya rasa Khafiat Adeleke.

"Tun daga nan har Legas, mutane suna kirana da Mejo Mejo''

"Kakata ce ta min su, saboda ni ɗaya ce tilo " in ji ta.

Ana yin wasu tsagun don kyau ne.

Tun Foluke Akinyemi tana yarinya aka yi mata na ta billayen.

Lambata-lambata ne masu zurfi a kowane kunci, kuma mahaifinta ne ya sa wani mai kaciya ya yi mata su.

"Mahaifina ya yanke shawarar yi min alamar ne kawai saboda yana ganin tana da kyau.

"Sun sa na yi fice kuma ina gode wa iyayena da suka min," in ji ta.

Labarin Akinyemi ya yi kama da na Ramatu Ishyaku daga Bauchi, a arewa maso gabashin Najeriya, wadda ke na ta zanen a gefen fuskarta kowanne.

"Don kyau ne," in ji ta, ta kara da cewa ta kuma yi wani ado a fuskarta a lokaci guda.

Ta kara da cewa tun tana yarinya irin wadannan alamomi na fuska sun shahara a can yankinsu, kuma ita da kawayenta ne suka je wurin wanzami domin a yi musu''.

Alamun fuskar Taiwo, wadda ta ba mu sunanta na farko kaɗai sun fara dusashewa, amma har yanzu bata manta yadda aka yi ta same su ba.

Lokacin da abokiyar tagwaitakarta ta mutu, sai Taiwo ta kamu da rashin lafiya kuma wani likitan gargajiya ya ba da shawarar a yi mata kwale don hana ta mutuwa ita ma.

Nan take ta fara samun sauƙi cikin ƴan kwanaki, amma hakan bai sa ta fara ƙaunar kwalen ba.

"Yana sa ka banbanta da kowa a cikin mutane, gwara a ce ba ni da shi kawai a fuskata,'' inji ta.

Akwai kuma irin su Murtala Mohammed da ke Abuja da ba su san labarin da ke tattare da nasu zanen ba.

"Kusan kowa a kauyenmu na jihar Neja yana da guda, don haka ban damu na tambaya ba," in ji shi.

Wanzamai irin su Umar Wanzam ne suke yin zane ko bille ta hanyar amfani da wuka mai kaifi.

Ya kwatanta shi a matsayin wani abu mai raɗaɗi da ake yi ba tare da maganin sa barci ko kawar da radadin ba.

Yawancin irin su Mista Akeem, wadanda aka yi wa zanen tun suna yara, sun yarda cewa ya dace a daina yin hakan.

Bai isar da al'adar ga 'ya'yansa ba ta hanyar yi musu suma.

"Ina son tsagun, amma sun dace ne da wani zamanin damar ba wannan ba''.