Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abdullah: Matashin da aka kashe a kan layin karɓar abinci a Gaza
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Panorama
- Lokacin karatu: Minti 7
Diaa, wani magidanci mai matsakaicin shekaru, mutum da ke ƙoƙarin daɗaɗa wa iayalansa a gidansa da ke ɗaya daga cikin sansanonin ƴangudun hijira a tsakiyar Gaza. To amma za ku ji baƙin cikin da ya shiga.
"Bismilla ku shigo ciki, wannan shi ne ɗakin Abdullah."
Abdullah shi ne babban ɗansa mai shekara 19. An harbe shi ranar 2 ga watan Agusta a cibiyar rabon abinci da Gidauniyar Rabon Tallafi ta Gaza(GHF), ke gudanarwa.
Cibiyar - wadda ake rabon abincin a kullum - ta ta fara aiki ne ciin watan Mayu.
Kuma isra'ila da Amurka ne suka kafa ta, kuma sojojin Isra'ilar (IDF) da kuma jami'an tsaron Amurka na musamman.
A cikin dakin Abdullah, wanda babu komai a ciki, Diaa ya sumbaci jakar dan ta zuwa makaranta.
"Allah sarki ɗana. har yanzu da ragowar ƙamshinsa a jikinta. Allah ya gafarta maka, ya yi maka rahma, ya sa aljanna firdausi ce makomarka, alfarmar Annabi Annnabi S.A.W.''
Diaa ya zargi kansa a mutuwar ɗan nasa. "Washe garin ranar da za a kashe shi, da daddare ya ke faɗa min cewa 'Baba zan je karɓo mana abinci gobe.'''
"Sai na ce masa, 'gaskiya ba na son ka je gobe, don haka kar ka je'''.
Amma sai ya ce ''Ina Allah ya yarda babu abin da zai faru, Baba.''
"Wallahi abin ya tsaya min a rai, ji nake kamar ni na yi sanadin mutuwar ɗana, sai na ji kamar ni ne na aike shi.''
"Tabbas muna buƙatar abincin. Na sadaukar da rayuwar babban ɗana domin ya ciyar da ƙannensa da kuma iyayensa.''
Gaza na fama da matsananciyar yunwa, sakamakon takaita shigar da abinci da sauran muhimman abubuwa da Isra'ila ta yi zuwa yankin
Lokacin da kawai ƙungiyoyin agaji da ƴankasuwa suka samu damar shigar da wadatattun kaya cikin Gaza, shi ne lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara ranar 19 ga watan Janairun wannan shekara.
Sai dai a ranar 2 ga watan Maris Isra'ila ta dakatar da shigar da kaya zuwa Gaza, sannan mako biyu bayan nan ta koma kai hare-hare.
Hukumar duniya da ke lura da buƙatar abinci ta gaggawa, IPC ta bayyana a cikin rahotonta na watan Agusta cewa Birnin Gaza na fama da ƙangin yunwa.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce babu yunwa a Gaza, tare da yin watsi da hujjojin da hukumar IPC da ya kira ''tsagwaron ƙarya''.
IPC, hukuma ce ta ƙwararru da duniya ta yarda ta ita a matsayin wadda ba ta ɗaukar ɓangare.
Mista Netanyahu ya ce Isra'ila ba ta da laifi kan ''ƙarancin'' abinci a yankin.
Ya zargi rashin gaskiya a hukumomin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a Gaza kuma ya sha zargin MDD da rashin yin kataɓus game da abij da ya kira shirya satar abinci da Hamas ke yi.
MDD ta musanta zarge-zargen nasa, tana mai cewa kayayyakin nata na da ƙayyadadun lambobi, kuma ana iya gano su.
Isra'ila ba ta taɓa gabatar da hujjoji kan zarginta na cewa Hamas na tsara sace abincin, duk da cewa MDD ta sha buƙatar hakan.
Ƙangin yunwa a Gaza shi ke sa mafi yawan matasan Falasɗinawa, kamar Abdullah, ke zaɓar jefa rayukansu cikin hatsari a cibiyoyin rabon tallafi na GHF don neman abinci.
A yanzu an kusan cika shekara biyu, tun bayan harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila tare inda ta kashe mutum 1,195, tare da yin garkuwa da mutum 251.
Har yanzu akwai ragowar 48 da ake ci gaba da tsare da su a Gaza, an kuma yi imanin cewa 20 daga cikinsu har yanzu na nan da ransu.
Harin ya kasance mafi munin abinda ya jefa Isra'ilawa cikin ƙuncin damuwa tun bayan samun ƴancin kan ƙasar a 1948.
Haka kuma martanin Isra'ila ya haifar da mafi munin damuwa da bala'i da Falasɗinawa suka fuskanta a cikin kusan shekara 80.
Isra'ila ta ci gaba da cewa matakin da take ɗauka na kare kai ne a Gaza - ƙaramin yankin da a yanzu ya rugujewa, inda aka kashe aƙalla mutum 65,000, ciki har da ƙananan yara 18,000, a cewar hukumar lafiyar Hamas a Gaza.
Isra'ila ta yi watsi da alƙaluman to amma hukumomin duniya da dama sun amince da su.
Abdullah yaro ne mai ƙwazo. Ya kafe wani rubutu a ɗakinsa da ke tuna masa ƙudirinsa na nasarar cin kashi 95 cikin 100 a jarrawarsa.
Makwabcin Abdullah, Moaaz, wanda abokinsa ne na ƙuruciya ya ba mu labarin abin da ya faru a ranar da ya mutu.
Tare da suka je cibiyar rabon abincin, GHF 4, wadda ita kaɗai ce a tsakiyar Gaza, ta hanyar bin ƙa'idar da dakarun IDF suka gindaya na zuwa cibiyar.
Domin zuwa cibiyar da wuri, Falasɗinawa kan yi sammako tun kafin ketowar asuba. Moaaz da Abdullah na jira a kusa da wani gida da ya rushe, ƙasa da tazarar mita 500 daga cibiyar.
Daga nan sai ƙaddarar ƙarar kwana ta dumfaro Abdullah, kawai sai suka ƙara matsawa, kamar mita 30 a cewar Moaaz.
A nan ne aka harbi Abdullahi. Moaaz ya ce nan take ya ruga da gudu domin samo sauran abokansu.
Diaa ya faɗa abubuwa masu yawa kan ɗan nasa, da yadda rayuwa a Gaza ke da matuƙar wahala.
"A baya muna rayuwa cikin kwanciyar hankali a Gaza. Abdullah matashi kamar sauran takwarorinsa masu jini a jika, bai samu damar cika burikansa na rayuwa ba."
BBC ta tuntuɓi rundunar IDF game da mutuwar Abdullah. Amma ba ta mayar da amsa ba, sai dai ta ce dakarunta ba sa buɗu wuta da gangan kan ''fafaren hular da ba su ji ba su gani ba''.
Lauyoyin GHF sun ce masu ba su kariyar tsaro ba sa buɗe wuta. Kyma sun ce ba su da masiya game da bayanin faruwar wani abu makamancin haka , sun kuma ce ba wanda ya taɓa harbi a cibiyar GHF ko kusa da ita.
Labarin Abdullah ya zo cikin wani film da muka naɗa kan abubuwan da suka faru a Gaza, kuma haska shi a baya-bayan nan da muka sanya wa suna Gaza: Yadda ake mutuwa saboda da abinci, wanda Panorama da sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC suka shirya.
Bincike ne kan halin yunwar da ake ciki a Gaza, da kuma zargin kashe-kashen da ake yi a cibiyoyin rabin abinci na GHF.
Shirin ya gudanar da binciken ne kawai kan ɓangare guda na bala'in jin ƙai a Gaza.
Mun gano yadda aka kashe Falasdinawa masu yawa a ƙoƙarinsu na neman a tallafi. Film din na da tsawaon kusan sa'a ɗaya da rabi.
Bayar da rahotonni da kuma shirya film na da matuƙar ƙalubale, saboda Isra'ila ba ta bai wa BBC ko wasu kafofin yaɗa labarai izinin tura wakilai zuwa Gaza domin bayar da rahotonni ba tare da matsala ba.
Ƴanjarida Falasdinawa da ke cikin Gaza sun yi gagarumin aiki, da ba don aikinsu ba, ba za mu san abin da ke faruwa a yankin ba cikin kusan shekara biyu da suka gabata.
A cewar ofishin jin ƙai na MDD, aƙalla 248 Isra'ila ta kashe daga cikinsu.
Wani jami'in IDF da muka zanta da shi ya kwarmata mana bayanai.
Amma ya buƙaci mu sakaya sunansa, saboda har yanzu yana aiki ada rundunar a matsayin jami'in jiran ko-ta-kwanaduk da cewa yana cike da shakku, kamar yadda sauran Isra'ilawa ke ciki ke ciki musamman game da abin da ake buƙatarsu da yi.
A lokacin da aka kira shi bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba, an gamsar da shi kamar yadda aka gamsar da sauran takwarorinsa cewa za su yi yaƙi ne domin kare ƙasarsu.
Amma yanzu yana damuwa kan cewa yana yaƙi ne domin kare buƙatar Netanyahu na ci gaba da kasancewa a kan mulki.
Mun ɓoye sunan sojan na ainihi domin kare shi, amma mun ba shi suna ''Micheal'' don wannan labari.
Ya yi magana a madadin wata ƙungiyar Isra'ilawa da ke adawa da mamayar yankunan Falasɗinawa tare da goyon bayan dakarun IDF da ke son yin magana kan abin da suka sani dangane da tilasta mamayar.
Michael ya kaɗu kan yadda zakuwa da yunwar da ya gani a Gaza.
"Yana da wuya a fahimci yadda muke wulakanta mutane da yanayin yunwa da tashin hankali game da abinci."
Ya ce an ba su umarni abin da ya kira ''buɗe wutar gargaɗi'', idan suna son kora mutane baya.
Sukan buɗu wuta idan mutane suka tsallaka layin da aka ware a cibiyoyin. Kuma ba a Falasɗinawan yadda tsarin yake ba.
"Akwia koren layi, akwai kuma jan layi. Idan suka haura koren za ku yi harbin gargaɗi, don haka za su gane ba a son zuwa nan sai su koma baya. Amma shi jan layin ya fi kusa da cibiyar, in suka zo nan kam za ka yi amfani da ƙarfi'', in ji Micheal.
Ya kuma shaida mana yadda yake matuƙar damuwa kan yadda IDF ke amfani buɗe wuta wajen isar da saƙo.
"Wallahi abin na damuna. Saboda ana fara harbin ba za su saurara ba, sai su fara gudu zuwa sansaninmu, daga nan sai mu fara tunanin yadda za mu yi da dubbansu.''
Michael ya ce cibiyoyin rabon agaji na GHF sun kasance masu tashin hankali kuma ba a tsara su yadda ya kamata ba. Amma ya ce cibiyar da yake aiki ba a taɓa harbin kowa ba, ''don haka mun yi sa'a''.
Rundunar IDF ba ta ba mu amsa kan tambayar da muka yi musu ba game da kabarin da Micheal ya ba mu kan kore da jan layuka.
kawai ta ce ta koyi darasi bayan ''samun rahoton illata fararen hula'' a cibiyoyin, kuma daga nan suka ''sabunta umarni kan dakarunsu da ke cibiyoyi.''