Ko haraji kan lemon kwalba zai iya rage illar cutar sukari a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Rahoto, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ciwon sukari na ɗaya daga cikin matsalolin kiwon lafiyar jama'a da ke haɓaka cikin sauri a duniya.
An tabbatar da cewa shan kayan zaki irin su lemon kwalba yana da alaƙa da taɓarɓarewar lafiya a cikin akasarin masu ciwon sukari da ma waɗanda ke kamuwa da cutar.
Masana kiwon lafiya suna bayar da shawarar cewa rage shan waɗannan kayan zaƙi, da cin ingantaccen abinci mai gina jiki, da ƙara yawan motsa jiki a matsayin dabarun inganta rigakafi da kuma daƙile ciwon sukari.
Najeriya na da kaso mai tsoka na kasuwar lemon kwalba da kayan zaƙi ta duniya kuma ana hasashen wannan kaso zai iya kaiwa na dalar Amurka biliyan 10 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2026 a kasar.
Wannan wata alama ce da ke nuna cewa yawan shan sukari a cikin abubuwan sha na zama matsalar lafiyar jama'a da ke buƙatar kulawar gaggawa da ke buƙatar kuɗaɗe masu yawa, wanda hakan ya sanya aka ɓullo da haraji na musamman kan lemon kwalba da sauran kayan zaki.
Girman matsalar ciwon sukari
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa yawan mutanen da ke fama da ciwon sukari a duniya ya tashi daga mutane miliyan 200 a shekarar 1990 zuwa miliyan 800 a shekarar 2022, kuma yaɗuwar cutar ya fi muni ne a ƙasashe masu tasowa.
WHO ta ƙara da cewa kimanin mutane miliyan 24 ne ke fama da ciwon sukari a nahiyar Afirka, kuma ana hasashen wannan adadin zai ƙaru da kashi 129 cikin ɗari zuwa miliyan 55 nan da shekarar 2045.
Afirka ta kasance nahiya ta biyu mafi ƙarancin kashe kuɗi kan batutuwan kiwon lafiya masu alaƙa da ciwon sukari, inda ake kashe dalar Amurka biliyan 13, wanda ya kasance kashi daya kacal na kuɗaɗen da ake kashewa kan cututtuka masu alaƙa da ciwon sukari na duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan matsalar na ƙara muni a Afirka ne saboda ba kasafai mutane suke sanin cewa suna da ciwon sukari ba saboda yana iya ɗaukar ɗan lokaci kafin alamominsa su bayyana, kuma idan har lokaci ya kai da waɗannan alamu suka bayyana cutar ta riga ta yi illa ga sassan jikin wanda ke fama da ita.
A Najeriya kimanin mutane miliyan 12 zuwa 14 ne ke fama da cutar kuma akasarinsu na buƙatar tallafi musamman daga gwamnati, kamar yadda mataimakin shugaban ƙungiyar masu fama da ciwon sukari ta Najeriya, (DAN) Dr Mansur Ramalan, ya bayyana:
''Ya zuwa yanzu dai babu wani tallafi da masu fama da wannan cutar ke samu daga gwamnati, kuma hakan ya samu cikin matuƙar damuwa domin mutane masu ciwon sukari suna buƙatar abinci na musamman, da magunguna da kuma sauran abubuwan gwajin yawan sukari a jini da dai sauransu, kuma yanzu komai ya yi tsada.''
Dr Mansur na magana ne a wani gangamin gwajin cutar sukarin kyauta da kuma wayar da kai kan larurar a Abuja a ƙarshen makon da ya gabata.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a ga cewa an ɓullo da hanyoyin da za a riƙa tallafa wa masu ciwon sukari domin su iya rayuwa da cutar ba tare da sun tagayyara ba.
Alaƙar lemon kwalba da ciwon sukari
Abubuwan sha masu zaƙi da lemon kwalba suna bayar da gudummawa ga haɗarin kamuwa da ciwon sukari, da kuma batutuwan da suka shafi sarrafa sukari da ke jinin mutanen da ke da cutar.
Jikin ɗan'Adam yana narkar da sukari da ke cikin lemon kwalba da sauri, kuma hakan yana bayar da gudummawa wurin rashin samun dadaito a yanayin sukarin da ake samu a jinin mutum.
''Bincike ya nuna cewa shan lemon kwalba yana haddasa ciwon sukari domin yana ƙara yawan sukarin da ke jikin mutum a lokacin wanda hakan ke sanya wa jiki ya sha wahalar sarrafa sukarin yadda ya kamata.'' In ji Dr Mansur.
Ya kuma ƙara da cewa yawan sukari a jikin ɗan'Adam na iya janyo wasu sauye-sauye a jikin mutum da za su iya haddasa ciwon sukari.
Ya ce: ''idan mutum yana yawan shan waɗannan abubuwan suna iya sanya shi ya yi ƙiba, kuma an san cewa ƙiba na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo ciwon sukari, saboda shi ke haddasa abin da ake kira 'insulin resistance' a Turance wanda yake kawo cikas wurin sarrafa abincin da ake ci kuma hakan sai ya kai ga mutum ya kamu da ciwon sukari.''
Mene ne harajin kayan zaƙi?
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi hasashen cewa daga shekarar 2011 zuwa 2030, asarar tattalin arziki da za a yi sakamakon ciwon sukari a duniya za ta kai adadin dalar Amurka Tiriliyan 1.7 inda ƙasashe masu tasowa a Afirka za su yi asarar dala biliyan 800.
Gwamnatocin ƙasashen na iya ɗaukar matakai da za su iya taimakawa musamman ta fannin samun ingantaccen abinci kuma su iya yin tasiri kan irin abincin da mutane ke ci.
Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake iya bi domin rage yawan amfani da lemon kwalba da mutane ke sha shi ne ɗora haraji kan kamfanonin da ke yin lemon na kwalba.
Kamar yadda ƙaƙaba haraji kan taba ya taimaka wajen rage yawan shan sigari a al'umma, sanya haraji kan abubuwan sha masu sukari zai taimaka wurin rage yawan sukarin da mutane ke sha.
Ƙasashe da dama a baya sun kafa dokoki da ke sanyawa ko ƙara haraji kan wasu nau'ukan abinci, irin su lemon kwalba da kayan zaki da cakulan, da nufin samun fa'idoji ta fannin ƙarin samun kuɗaɗe da kuma inganta kiwon lafiya.
A baya bayan nan, ƙungiyar masu fama da ciwon sukari a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta dawo da harajin da ta dakatar da ake karɓa daga kamfanonin lemon kwalba, domin ta haka ne za a iya samun kuɗaɗen da za a iya taimaka wa masu fama du cutar.
Dr Mansur Ramalan ya bayyana cewa ganin halin matsin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya masu fama da wannan cuta za su yi maraba da duk wani irin tallafi da za su iya samu.
Ya ce: ''Wannan haraji na iya taimaka mana sosai domin idan aka yi la'akari da magani kamar Insulin, yana ɗaya daga cikin magunguna da masu wannan cutar ke yawan amfani da shi.
Gwamnati na iya taimaka wa a rage farashin allurar ko kuma ta ma sayi allurar ta ba wa masu cutar kyauta, kamar yadda ake yi a ƙasar Masar inda ake bai wa ƴan kasa da shekara 18 allurar ta Insulin kyauta.''
Abu mafi muhimmanci da ya kamata gwamnatoci su yi la'akari da shi, shi ne domin rage shan sukari a al'umma da kuma daƙile yaɗuwar annobar mummunar ƙiba da ciwon sukari, akwai buƙatar ɓullo da tsare-tsare da za su wayar da kan jama'a kan illolin wasu nau'kan abincin da suke ci domin haka na da matuƙar tasiri kan ingancin lafiyarsu.











