'Wahalhalun da nake sha bayan yanke min ƙafa saboda ciwon suga'
Duk shekara a rana irin ta yau – ta Wayar da Kai Kan Ciwon Suga – duniya kan mayar da hankali kan ƙalubalen da masu cutar ke fuskanta. A wannan shekarar, hankula sun koma kan Afirka, nahiyar da cutar ke ƙara ƙamari.
Taken ranar ta wannan shekara shi ne “Kawo Ƙarshen Ƙalubale, Cike Gurbi” wato Breaking Barriers, Bridging Gaps a Turance, kuma an ƙirƙire shi ne da zimmar inganta hanyoyin samun magani ga miliyoyin masu cutar.
Bayanai sun nun cewa a Afirka, kusan mutum miliyan 24 ne ke fama da cutar a yanzu. Sai dai abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yadda aka yi hasashen adadin zai ninninka cikin sauri.
Zuwa 2045, manyan mutanen da ke ɗauke ciwon suga a Afirka za su ninka, inda za su kai miliyan 55 – ƙarin kashi 129 kenan.
Duk da wannan ƙaruwa, kashi 46 cikin 100 ne kawai na masu ciwon suka san halin da suke ciki.
A faɗin duniya, sama da manyan mutane miliyan 537 ne ke rayuwa da ciwon, kuma ana san za su ƙaru zuwa miliyan 783 nan da 2045.
Mutane da dama da ke fama da matsalar na kokawa kan irin wahalhalu da suke fuskanta, musamman wajen sayen magani.
Wani mai fama da lalurar da ke zaune a jihar Nasarawa ta tsakiyar Najeriya, Zubairu Tanko Sulaiman, ya bayyana wa BBC irin halin da ya shiga sakamakon kamuwa da cutar.
Ya ce ya fara kamuwa da ciwon ne bayan dawowarsa daga Saudiyya a shekara ta 2002, inda ya shafe shekara 24 yana fama da shi.
Tsadar magungunan cutar

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin matsala da Zubairu Tanko ya ce yana fama da shi, shi ne tsadar maganin ciwon na suga.
Ya ce magungunan cutar sun tashi matuka, musamman ma allurai.
"Maganin ya fara tashi tun shekara ta 2017 zuwa 2018. A baya ina sayen magunguna da yawa na ajiye, amma yanzu ba zan iya yin haka ba," in ji Zubairu.
Ya ce a can baya yana sayen maganin (insulin 70-30) kan naira 800, amma yanzu ya tashi zuwa 12,000.
"Idan kana da kuɗi ba za ka samu matsala ba, in kuma babu za ka ɗanɗana kuɗarka," in ji shi.
Ya ce lalurar ta suga ta fara kamari ne a 2015.
Yanke ƙafa

Asalin hoton, Getty Images
Zubairu ya ce ciwon ya janyo masa nakasa inda yanzu ba ya iya fita ya yi abubuwan da ya saba yi a baya.
Ya ce ta canza rayuwarsa ba kaɗan, inda ya ce a baya yana iya fita domin neman abin sakawa a baki, amma yanzu ba ya iya hakan.
"Lokacin da nake da karfi ina iya fita domin yin aiki. Amm yanzu abin da zan ci da yara ya fi karfina. Har kafa na rasa sakamakon ciwon suga," in ji Zubairu.
Ya ce wasu mutane ne ke taimakonsa saboda ba ya iya taɓukawa kansa komai a yanzu.
Matsananciyar damuwa
Mutumin mai fama da ciwon na siga ya ce wani abu da lalurar ke saka shi, shi ne damuwa da kuma tunani a wasu lokuta.
"Watarana in na zauna har hawaye nake yi ganin halin da na shiga saboda lamarin ya sauya rayuwata.
"Amma ina gode wa Allah saboda haka ya tsara min," in ji Zubairu.
Sai dai ya ce duk da halin da ya shiga ba ya yin bara saboda bai iya ba.
Ya ce bai bari matsalar ta saka masa ciwon hawan jini ba, inda yake iya ƙoƙarinsa wajen yin tawakkali da abin da ya same shi.
"Duk lokacin da na ga zan kamu da hawan jini sai na tashi da daddare na gode wa Allah kan abin da ya yi min, musamman na yanke kafa," in ji shi.
A ɗaya gefen, ya gode wa mutanen da suka taimaka masa a baya da kuma suke ci gaba da yi har yanzu.












