Za a kara tsakanin Spain da Brazil a Santiago Bernabeu

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya da ta Brazil sun sanar da cewar za su buga wasan sada zumunta a tsakaninsu cikin watan Maris a Santiago Bernabeu.
Taken wasan shi ne ''Kalar fata iri daya'' domin yaki da wariyar launin fata da cin zarafin ƴan wasa da ake fama a wasannin gasar Sifaniya.
Za a buga karawar ranar 26 ga watan Maris a filin wasa na Santiago Bernabeu, karo na 47 da tawagar Sifaniya za ta taka leda a filin.
Kafin nan Brazil za ta buga wasan sada zumunta da Ingila ranar 23 ga watan Maris, sai kwana uku tsakani ta ziyarci Sifaniya.
Haka kuma Brazil za ta kara a wasan sada zumunta da Mexico ranar 7 ga watan Yuni.
Sifaniya za ta yi wasa da Brazil a shirin fuskantar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Jamus, wadda za ta fara da Croatia ranar 15 ga watan Yuli.
Ita kuwa Brazil tana buga wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.
Brazil za ta karbi bakuncin Equador ranar 4 ga watan Satumbar 2024 a wasa na bakwai a cikin rukunin Kudancin Amurka.
Brazil, wadda ta yi wasa shida mai maki bakwai tana ta shidan teburi, inda Argentina take jan ragama da maki 15.











