Biden ya ce ya haƙura da takara ne domin haɗin kan Amurka da jam'iyyarsa

Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu wani abu da ya fi cetar dumukuradiyya muhimmanci hatta burin mutum na kanshi.

Biden ya ce ya hakura da takarar sake neman shugabancin ne domin ya hada kan kasar da kuma jam’iyyarsa ta Democrat.

Matakin na sa ya sa yanzu mataimakiyarsa Kamala Harris ta kama hanyar zama ‘yar takarar jamiyyar, inda kuma abokin hamayyarsu Donald Trump ya caccake ta da cewa ba ta dace ba.

A jawabin da Biden ya yi a ofishinsa da ke fadar gwamnatin kasar, wanda aka yada ta talabijin ya ce ya yanke shawarar ajiye takarar neman sake zabensa ne, domin babu abin da ya kamata a ce ya fi muhimmanci fiye da kare dumukuradiyya.

Shugaban wanda kafin ya yi hakan yake ta shan matsin lamba daga jiga-jigan jamiyyarsa kan ya hakura da takarar ganin yadda ya kasa tabuka abin a-zo-a-gani a muhawararsu ta farko ta dan takarar Republican, tsohon shugaban kasa Donald Trump, ya ce ya yi hakan ne domin hada kan kasar da kuma jamiyyarsa ta Democrat.

Kuma ya ce wannnan mataki da ya dauka yanzu zai haifar da makoma ga Amurka da ma duniya a gomman shekaru nan gaba.

Biden mai shekara 81, ya kara da cewa yanzu lokaci ne na matasa kuma abin da ya fi dacewa shi ne mika akalar jagorancin ga sababbin jini.

Ya yaba wa mataimakiyarsasa Kamala Harris, wadda ya zaba domin ta samu takarar zaben na watan Nuwamba, wadda kuma ke kan gaba wajen zama ‘yar takarar ta Democrat da cewa kwararriya ce da ta dace da kuma cancanta.

Biden ya ce yanzu ya rage ga al’ummar Amurka su sama wa kasar makoma da ta fi dacewa.

Ana ganin jawabin shugaban ba zai sa masu sukarsa ‘yan Republican da ke cewa idan dai har ba zai iya sake yin takarar ba to bai kamata ma ya ci gaba da zama a kan kujerar shugabancin kasar ba.

Mista Biden ya kuma ce zai ci gaba da wanzar da manufofinsa na cikin gida da kuma waje a ragowar lokacin mulkinsa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ita kuwa mataimakiyar tasa tun bayan da ya sanar da cewa ya hakura da takarar a ranar Lahadi, ta tashi tsaye ba zama ta kama yakin neman takarar ta jam'iyyarta ba ji ba gani.

Yanzu dai abin da ya rage a gani shi ne yadda Biden din zai dafa mata wajen ganin ta kayar da Trump, a zaben na watan Nuwamba.

A gangamin yakin neman zabensa na farko tun bayan da Kamala Harris din ta zama wadda ake ganin za ta kasance abokiyar hamayyarsa a babban zaben, ya caccake ta a jawabinsa a North Carolina.

Ya bayyana ta a matsayin mafi rashin dacewa, kuma mataimakiyar shugaban kasa mai tsattsauran ra’ayin gaba-dai-gaba-dai a tarihin Amurka.

Ya soki manufofinta a kan ‘yancin zubar da ciki da mallakar bindiga sannan ya zarge ta da gazawa a kan batun baki kuma ya dora mata alhaki kan matsalar hauhawar farashi a kasar.

Ya ce: ''A matsayinta na mataimakiyar shugaban kasa, ta kada kuri'ar da ta haifar da hauhawar farashi mafi muni a cikin rabin karni, ta gurgunta iyalai masu tsaka-tsakin samu, ta yi musu illa sosai kamar yadda dukkanninku kuka sani al a North Carolina.''

Haka kuma Trump ya ce makiya dumukuradaiyya ne a jagororin jam'iyyar Democrat suka fitar da Biden daga takara.