Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu ke tsangwamar mata masu juna biyu?
- Marubuci, شمائلہ خان
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, صحافی
'Idan na ƙara kiba ba na damuwa. Ina cike da farin ciki.' Waɗannan kalaman wata ce Rasti Saeed, ta kasance mai motsa jiki da ta zama uwa karon farko a bara.
Ta ce farin cikin da ta shiga ba zai misaltu ba lokacin da ta ɗauki juna biyu, sai dai mutane sun yi ta maganganu kan kiba da ta yi.
'Wasu mutane sun sha faɗa min cewa kiba ta ta yi yawa, har da cewa in riƙa rufe jikina gaba-ɗaya don ba shi da kyau, ka da ki nuna cikinki, ki saka babban tufafi.'
Ba ita kaɗai ba ce ke fuskantar irin waɗanan kalamai daga wajen mutane bayan samun juna biyu.
A cewar Asusun Kula da Yawan Al'umma na MDD, ya ce yara kusan miliyan 5.6 ne ake haifa kowace shekara a Pakistan.
Lokacin samun juna biyu, yanayin jikin mata na sauyawa, saboda suna fuskantar abubuwa daban-daban, sai dai kalaman wasu mutane sukan firgita su.
Tauraruwar fina-finai mai suna Maryam Ansari ta haifi yaronta na farko a wannan shekara.
Ta ce lokacin da take ɗauke da juna biyu, an faɗa mata cewa 'kada ki ci burodi', za ki yi kiba, kada ki ci shinkafa, za ki rasa gashinki, idan kika haifi yaro, za ki gani, ban saba ganin haka ba.
An takaita wa mata yin tafiye-tafiye lokacin juna biyu, ba tare da la'akari daga inda suka fito ba.
Samin Nawaz ƴar jarida ce kuma ta shiga wata ƙungiya bayan ta haihu.
"Ga mata, an yi tsammanin cewa yanzu da suke cikin wannan mataki, su tsaya iya wurare da aka kayyade, kada su nuna jikinsu ga duniya," in ji Samin.
"Ban san lokacin da samun juna biyu ya zama laifi ko rashin tarbiya ba"
Malamar mai koyar da motsa jiki, Rasti Saeed na gudanar da cibiyarta a tsakiyar birnin Karachi na Pakistan.
Ta ce lokacin da take ɗauke da ciki, ta ji abubuwa da dama.
A cewar Rasti, 'dole ne za a yi magana. Mutane sun faɗa cewa ƙuguna ya girma, yarinyar tafi ni girma, kada ki yi tafiya da yatsun kafa, mahaifa za ta sauka.'
Rasti ta kuma tuno wani al'amari inda wani gidan talabijin ya naɗi wani shiri da ita lokacin da take da juna biyu, sai dai ba a watsa hirar ba.
A cewar hukumomin gidan talabijin ɗin, bai kamata a haska shirin ba saboda tana ɗauke da juna biyu.
Rasti ta ce wani ma'aikacin gidan talabijin ya ce bai dace su watsa shirin ba saboda tana da juna biyu. Na kaɗu matuka, mene ne laifin haka?
Mene ne laifi da ba za a nuna shirin ba?' Lokacin da Rasti ta yi rubutu a kan al'amarin a shafukan sada zumunta, ta samu gagarumar goyon baya daga wajen mutane kuma gidan talabijin ɗin ya koma gayyatarta a kai-a kai cikin wani shiri domin tattaunawa a kan maganar camfe-camfe da ke alaƙa da zama uwa.
Bayan ta haifi ƴarta, tauraruwa Maryam Ansari ta yaɗa hotunan lokacin da take da juna biyu a shafukan sada zumunta, ta samu martani mara kyau da sakonnin da suka sanya ta goge shafukanta na soshiyal midiya.
Maryam ta saki wani bidiyo na mayar da martani inda take cewa, 'Ban san lokacin da ya zama laifi ba ko rashin tarbiya samun juna biyu. Kowa haihuwar shi aka yi.
'Idan mace ta samu juna biyu, ku taya ta murna da kuma yi mata addu'a.'
Da take zantawa da BBC, Maryam ta ce ta ɗauki hotunan da take da juna biyu sanye da tufafin da ya rufe ɗaukacin jikinta don tuno da lokacin kafin ta haifi ƴarta ta fari.
'Lokacin da aka haifi Amaya, na yi tunanin cewa wata dama ce mai kyau ta sanar wa dukkan masoyana a shafukan sada zumunta cewa na gode Allah da samun ɗiya da na yi.'
Sai dai an ɗauki hotunan da ta yaɗa a matsayin abu mara kyau, an yi mata ba'a tare da mayar da farin cikinta zuwa bakin ciki.
Ta faɗa cewa mutane da dama sun tura mata sakonnin fatan alkhairi, sai dai waɗanda suka zage ta su suka fi yawa.
'Idan na samu suka da yawa, ina shiga hali mara kyau.'
Ƴar jarida Sameen Nawaz ta koma ofis bayan haihuwa.
Ta ce 'muna da wasu mutane a ɓangarenmu da ke nuna cewa idan mutum ya ƙasa shawo kan al'amura, to yayi shi ta hanyar rufe jikinsa.'
"Aikin gida yana da matukar wahala"
Ko da mace mai ciki na jin kunyar kiba da take yi sakamakon kasancewa cikin ado da kwalliya da al'umma ke so.
Mata da yawa ne batun tsangwama ke shafa a cikin al'umma.
Sameen Nawaz ta ce lokacin da ta sauya aiki daga watanni shida zuwa takwas, hakan ya shafi kuɗaɗen da take samu, amma ta ƙara jajircewa wajen yin aikin.
Rasti Syed ta ce, 'Za ka gamu da kalamai marasa kyau daga ko'ina, to amma a lokacin ina cike da farin ciki don haka abin bai shafe ni ba.'
Tauraruwar fina-finai Maryam Ansari ta yi imanin cewa 'mace tana da karfi' kuma ta gane haka ne lokacin da zama uwa. Maryam ta yi aiki fiye da kwanakin da ake buƙata lokacin da take ɗauke da juna biyu.
"Na fara yin sana'ata, na buɗe situdiyo tare da mijina, na yi aiki, na koyar, na kammala karatun digiri a ɓangaren lauya, na ɗauki hotunana da kuma yaɗa su, ina ganin a wata na tara na ɗauki hutu.'
Ta ƙara da cewa 'akwai mata da yawa irina waɗanda su ma ke aiki bayan haihuwa, da kula da aikin gida kuma ina son in faɗi wani abu cewa aikin kula da gida shi ne mafi wahala.'