Yakin Ukraine: Rasha ta kai hari cibiyar makamashin nukiliyar Ukraine mafi girma a Turai

Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya zargi Rasha da dawo da yaƙin ta'addanci nukiliya bayan makaman da dakarun Rasha ke harbawa suka fada a kan cibiyar makamashin nukiliya mafi girma a nahiyar Turai.

A wani sakon bidiyo Mista Zelensky ya zargi Moscow da neman maimata bala'in Chernobyl, yayin da take zafafa hare-hare a Zaporizhzhya da ke kudancin Ukraine.

Mahukunta Ukraine sun ce an kashe wutar da ta tashi a cibiyar da samun raguwar hayakin da ke fita, bayan wani bangare na cibiyar ya kama da wuta.

Magajin garin na Enerhodar da ya bayyana cewa wannan cibiya ita ce mafi girma a Turai, ya roki Rasha ta daina musu luguden wuta, saboda wannan yanayi babban bazarana ce ga tsaron duniya.

Shugaba Volodymyr Zelensky ya jadada bukatar dole Turai ta tashi tsaye domin kare cibiyar makamashin nukiliyar mafi girma da aka kai wa hari.

Ya ce da gangan Rasha ta kai hari kan wannan cibiya domin tankokin da ta fi amfani da su wajen kaddamar da harin na dauke da kamarori da ke nuna inda ake son harbi.

Mista Zelensky ya ce Rasha tana sane da duk abin da take yi kuma wannan hari dama ta tsara shi ne.

Hukumar da ke sa ido kan nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce na'urorinta masu muhimmanci ba su kama da wuta ba. Sai dai kwararru na cewa ba a taɓa ganin inda aka kai irin wannan hari kan cibiyar nukiliya ba, kuma har yanzu akwai sauran barazana.

Tsohon shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya shaida wa BBC cewa 'yan kasar a shirye suke su ci gaba da nuna jajircewa.

Mista Poroshenko ya ce; "Ba za mu rasa Mariupol ba, ba za mu rasa Kharkiv ba, ba za mu rasa Kyiv ba. Putin ka manta da wannan tunani. Kasa ce baki daya ke yakar Putin domin haka ba za ka iya mana kawanya ba, ko ka jefa mu cikin duhu ko ka kashe rayukan 'yan Ukraine ba.

"Ba ma tsoron Putin, za mu dakatar da Putin, mun yi imani da karfin makaman da ke hannunmu, kuma ba za mu bari Putin ya sake danno kai ba."

A yanzu dai shugaba Zelensky ya tattauna da shugaba Biden, wanda ya roƙa ya mara masa baya ta hanyar umurtar Moscow ta tsaigata ruwan wuta a Ukraine saboda bai wa jami'an agaji damar kai dauki.

Ya kuma tattauna da Firaministan Burtaniya Boris Johnson wanda ya ce shi ma zai nemi a gudanar taron gaggawa na kawamitin tsaro na MDD nan da sa'o'i kadan.

Ƙasashen duniya dai na ci gaba da alla-wadai da wannan yaƙi da kuma yadda Rasha ke kin sauraron bukatar tsaigata wuta.