Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kashe tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara

Asalin hoton, FACEBOOK POST
Rahotanni sun ce 'yan bindiga dauke da makamai sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.
Bayanai sun ce an samu asarar rayuka ciki har da wani tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.
'Yan uwan marigayin sun tabbatar wa BBC Hausa faruwar al'amarin kuma sun ce ya gamu da ajalinsa ne lokacin da 'yan bindigar suka tare hanya.
Malam Mohammed Sirajo Hamidu ƙanin marigayin ne kuma ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun buɗe wuta ne lokacin da direban yayansa ya yi ƙoƙarin juyawa domin komawa Kaduna bayan da suka fahimci cewa sun faɗa tarkon masu garkuwa da mutane.
"Masu garkuwa da mutane ne suka tare hanya kuma suna zuwa sai suka tarar da abin da ke faruwa, ganin haka sai suka yi sauri suka juya, suna juyawa za su koma Kaduna sai wasu mutum uku suka fito daga cikin daji suka tsaya a gabansu su ka buɗe wa motarsa wuta, harsashi daya ya same shi a ƙirji, daya kuma a kafarsa".
Ya kuma ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da jami'in dan sanda daya da ke tsaron lafiyar marigayin ya yin da dirbarsa ya kubuta
Sai dai duk da cewa kawo yanzu ba a san adadin mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su ba amma hotunan da wasu matafiya suka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motoci da dama a kan hanya kuma ba bu kowa a cikinsu.
Wasu bayanai sun ce adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya kai 40.
Shafin PRNigeria ya ambato wani matafiyi da ya kuɓuta yana cewa 'yan bindigar sun tare hanya a ƙauyen Katari da misalin ƙarfe biyu na rana inda suka shafe sama da sa'a guda suna ɓarna.
Matafiyin ya ce "Sai da muka koma bayan da muka ji harbe-harben bindiga kuma mun tsaya a wani wuri mai tazara sosai da wurin da al'amarin ya faru.
"Bayan sa'o'i biyu mun ga wasu motoci na bin ɗaya hanyar, daga nan mun ci gaba da tafiyarmu".
"An yi garkuwa da matafiya da dama ko sun tsere cikin daji saboda mun ga motoci aƙalla 15 a kan hanya kuma ba bu kowa a cikinsu lokacinda da muka wuce wurin da al'amarin ya faru," in ji shi
Sai dai har yanzu rundunar ƴan sanda jihar Kaduna ba ta ce komai kan al'amarin.
Kauyen Katari na daya daga cikin wuraren da masu garkuwa da mutane ke tasiri a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ko a baya ma sai da yan bindigar suka yi garkuwa da Sarkin Bungudu na jihar Zamfarar Mai Martaba Hassan Atto.
Ya kubuta daga hannun ƴan bindigar bayan ya yi kwanaki 32 ana garkuwa da shi.










