Jihar Neja: An haramta sayar da 'Boxer' da 'Jingchen' da wasu nau'in babura a jihar

..

Asalin hoton, FACEBOOK

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya haramta sayar da babura a jihar sakamakon matsalolin tsaro da kuma yadda ƴan bindiga ke buƙatar a kai musu baburan a maimakon kuɗin fansa na karɓar waɗanda aka sace.

Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane ne ya sanar da hakan a wata sanarwa inda sakataren ya ce cikin baburan da aka hana sayarwa akwai Bajaj da Boxer da Qiujeng da Honda da ACE da Jingchen waɗanda ƙarfin injinsu ya kai 185cc zuwa sama.

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma ce an ƙiƙiro waɗannan matakan ne domin hana ƴan bindiga saƙat a jihar.

Matane ya kuma ce gwamnatin jihar na sane da halin da jama'a za su shiga sakamakon waɗannan matakan amma an ɗauke su ne saboda kare jihar inda ya yi kira ga dillalan baburan da su bayar da haɗin kai.

Haka kuma ya buƙaci jama'ar jihar da su ba gwamnati haɗin kai domin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da suka addabi jihar.

Jihar Neja dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da yan bindiga ke cin karensu ba babbaka.

A bana dai ƴan bindigan sun gudanar da aika-aika iri-iri daga ciki har da sace ɗaliban makarantar Kagara da kuma ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko Yakasai.

Haka kuma sun yi garkuwa da mutane da dama da kashe su da sace dukiyoyinsu da dabbobi a ƙauyuka daban-daban.