Son ƙazamar riba ya sanya ƴan kasuwa ɓoye mai – NNPC

Asalin hoton, Other
Kamfanin man fetur na Najeriya - NNPC ya musanta zargin da ake cewa yana shirin ƙara farashin litar mai a ƙasar.
Shugaban NNPC, Malam Mele Kyari a hirarsa da BBC ta wayar tarho, ya bayyana cewa ƴan kasuwa ne suka jawo dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassan ƙasar bisa tunanin idan an ƙara kuɗin sai su ci riba mai tsoka.
"Abin da ya sa ake ganin waɗan nan layukan shi ne ajiye kayan da mutane suka yi da suka daina sayar da man da waɗansu gidajen man da suka sayi man suka daina saidawa ko suka rage saidawa". in ji Kyari.
A cewar shugaban NNPCn, kamfanin ba shi da ƙudirin ƙara farashin a wannan watan na Maris. Ya kuma ce gaskiya ne batun da ake cewa ƙarin farashin gangar mai na da nasaba da fargabar da mutane suke na cewa za a iya ƙara farashin man.
Ya bayyana cewa "Cikin halin da ake ciki yanzu, idan aka ce za a sayar da man kamar yadda kasuwa ta kama, lalle ya fi naira 160 da ake saidawa, amma kuma tallafi ne da gwamnati take sa wa a kan kuɗin man kuma wannan shekarar babu cikin kasafin kuɗin bana".
Shugaban kamfanin man na Najeriya ya ce suna ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago da sauran ƙungiyoyi da gwamnoni domin ƙayyade farashin da ba zai bai wa talaka wahala ba.
A faɗarsa, duk da janye tallafin man, gwamnati za ta ƙyale ƴan kasuwa su sa farashi amma tare da sa idon hukuma saboda "shi ake yi a kowace ƙasa, duk duniya shi ake yi kuma tsarin da ake don a tabbatar da cewa ba a cutar da talaka ba".
Ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da kuɗaɗen tallafin man wajen gina tituna da makarantu da asibiti.

Ina aka kwana game da tace man fetur a Najeriya?
Shugaban na NNPC ya ce matakin farko shi ne fara gyaran matatun man fetur na ƙasar sannan aikin ya yi nisa kuma hakan, a cewarsa, zai ba da damar samun isasshen man fetur a ƙasar.
Ya bayyana cewa "akwai manya-manyan matatun mai da ake ƙerawa da kuma wasu ƙananu da ake yi wanda a haɗe idan an dunƙule su zuwa shekara biyu ko uku, za a daina shigo da mai daga kowace ƙasa zuwa wannan ƙasa"
Malam Mele Kyari ya ƙara da cewa tsarin zai kawo rangwami a farashin man domin "idan aka siyo shi daga waje, sai an sa jirgin ruwa da sauran kuɗaɗen da dole sai an biya kafin a kawo man wannan ƙasar".

A ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 ne ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci 'ya'yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.
Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.
Tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulkin Najeriya, an yi ta samun ƙarin kudin man fetur a lokutan daban-dana, kamar dai yadda ya sha faruwa a gwamnatocin baya.
Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai a ƙasar ba, hakan ya tayar da hankalin mutane da dama.










