Abin da matar da ta rasa yara huɗu a fashewar Zamfara ta gaya wa BBC

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar ƙauyen Magamin Diddi na ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da alhinin rashin 'ya'yansu bakwai da suka mutu sakamakon fashewar wani bam.
Lamarin dai ya faru ne bayan yaran sun tsinci abin fashewar wanda mutanen garin suka ce sojoji ne suka jefa wa 'yan fashin daji, amma bai fashe ba.
Yaran su kimanin tara da suka je gona don yin kara, sun tono bam ɗin, inda ya tashi da su, kuma ya yi sanadin mutuwar wasu nan take, daga bisani kuma wasu suka cika a asibiti.
Mahaifiyar da ta rasa ƴaƴa huɗu a lamarin ta shaida wa BBC cewa tsautsayin ya shafi ma waɗanda a baya ba sa zuwa yin kara.
"Na yi surfe da ni babban, ɗan ƙaraminsu cikon na biyar sai na aza mai ya kai wajen niƙa kafin sauran su dawo daga wajen kara," in ji ta.
Ta ce bayan nan ne suka jiyo ƙarar wani abu ya tashi kuma ƙura ta turnuƙe, guguwa ta tashi "sai ga wata yarinya wadda Allah Ya hukunce ta kawo labarin, sai ta rugo da gudu" domin sanar da mutuwar yaran.
Daga baya kuma mutanen gari suka buƙaci yarinyar ta kai su wajen da lamarin ya faru inda kuma aka ga wasu daga cikin yaran da ransu wasu kuma tuni rai ya yi halinsa.
"Wasu an kai asibiti waɗanda da sauran ransu da wasu ba a kai su asibiti ba suka mutu wasu kuma suna asibiti" in ji ta.
Matar ta ce abin da take iya tunawa na ƙarshe da yaran shi ne "da safiya ta waye ba ni da ruwa na tara su na ce kowa ya je ya ɗebo min ruwa na samu na wankin baki, kuma da za a wurin kara duk kowa sun warwatse na kira kowa na ce su taho su tafi wurin kara".
A cewarta, duk da mutuwar yaran ta taɓa ta ƙwarai amma tuni ta ɗau danganar rashin su.
Ku latsa alamar lasifikar da ke ƙasa domin jin bayanin da mahaifiyar yaran ta yi wa BBC.
Kwamishinan Tsaro na Zamfara, Abubakar Dauran, ya ce akwai yiwuwar jami'an tsaro ne suka jefa abin fashewar yayin wani hari da suke kaiwa kan 'yan fashin daji da suka addabi jihar.
Tuni aka yi jana'izar yaran kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a cewar Abubakar Dauran.












