Buhari ya yi tir da rikice-rikicen ƙabilanci a Najeriya

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kare dukkan mabiya addinai da dukkan ƙabilun kasar - ko da kuwa suna da rinjaye a yankin da suke rayuwa - ko kuma tsiraru ne su, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Cikin wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai ba shugaban Najeriyar shawara kan kafofin yaɗa labarai ya fitar a jiya Lahadi, Shugaba Buhari ya mayar da martani kan rahotannin barkewar rikici a wasu sassa na kasar, rikicin da wadanda shugaban ya kira "kungiyoyi da ke da alaka da na kabilanci da na bangaranci" suke haddasa wa.

Shugaba Buhari ya gargadi irin wadannan kungiyoyin cewa gwamnatinsa ba za ta kyale su su ci gaba da rura wutar kiyayya da tashin hankali kan wasu jama'ar kasar ba.

Sanarwar ta kuma ce shugaban ya yi tir da rikce-rikicen kuma ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamantinsa za ta dauki matakan da su ka dace domin kawo karshen wadannan tashe-tashen hankulan da ke karuwa a cikin kasar.

Duk da cewa shugaban Najeriyar bai ambaci wani yanki ba cikin sanarwar da ya fitar, amma ana ganin yana magana ne a kan rikicin kabilancin da ke aukuwa a birnin Ibadan da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Ondo State ethnic inspired attacks on Hausa and Fulani groups

Asalin hoton, TWITTER/ONDO STATE APC

Wannan rikici ne tsakanin Yarabawa da Hausawa 'yan kasuwa a birnin na Ibadan - a wata kasuwa Shasha ta unguwar Akinyele, wanda zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton, rikicin ya lakume rayuka 10 da asarar dukiyoyin Hausawan da su ka kasance tsiraru ne a yankin.

A karshen sanarwar, shugaban ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya da gwamnonin jihohi da sauran shugabanni na siyasa da jama'a su ka zaba daga sassan kasar, da su hada hannu da gwamnatin tarayya domin tabbatar da al'umomin da ke yankunan da su ka fito ba su dare gida-gida ba saboda dalilai na bambancin kabila ko wasu dalilai kamar na bangaranci da na addini.

'A daina kashe 'yan Arewa'

Tun bayan rahotanni sun watsu kan rikicin da ya barke a Ibadan ne mutane daban-daban suka rika yin kira-kiraye a shafukan zumunta kan a daina rikicin.

Tun da safiyar yau Lahadi ne masu amfani da dandalin Twitter musamman 'yan arewacin kasar suka riƙa amfani da maudu'in #stopkilingnortherners wato a daina kashe 'yan Arewa.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an ambaci maudu'in sau fiye da 10000.

"Kisan 'yan Arewa da ba su ji ba ba su gani ba abin takaici ne," a cewar mawaƙi Umar M. Shareef maƙale da maudu'in #stopkilingnortherners.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi kuwa Suraj tambaya yake cewa "me ya faru da maganar ƙasa ɗaya dunƙulalliya cikin 'yanci da kwanciyar hankali?".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi tur da "hare-hare a kan 'yan Arewa da ke kasuwancinsu a kasuwar Sasa wanda ya jawo kashe-kashe" sannan ta yi kira da a yi bincike kan lamarin don yin adalci.