Yadda aka ‘kashe mutum 10’ a rikicin Hausawa da Yarbawa na Ibadan

Asalin hoton, @OndoAPC
Wani shugaban Hausawa da ke Jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya ya tabbatar cewa mutum 10 ne suka mutu sakamakon hare-haren da wasu ɓata-garin Yarabawa suka kai wa Hausawa.
Lamarin ya faru ne bayan mutuwar wani Bayarabe a kasuwar Shasha sakamakon hatsaniyar da ta ɓarke tsakanin wani Bahaushe mai turin baro da wata Bayarabiya mai shago a kasuwar ranar Alhamis.
Ganau sun ce Bahaushen, wanda ke tura baron tumatur, ya faɗi a gaban shagon matar abin da ya sa tumaturin ya zube. Hakan ne ya sa matar ta ce dole ya tsince dukkan tumaturin, lamarin da ya kai ga rikicin da ya yi sanadin mutuwar wani Bayerabe.
"Daga nan ne wasu 'yan banga na ƙabilar Yarabawa suka far mana sakamakon hatsaniyar a kasuwar Shasha," a cewar wani mutum da ke samun mafaka bayan rikicin.
Ya ƙara da cewa "lamarin ya yi sanadin mutuwar wani dan uwan matar - shi ya sa Yarabawa suka fantsama lungu da saƙo suna kai wa Hausawa hari".
Sai dai shugaban Hausawan kasuwar Shasha, Alhaji Usman Idris Yako, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu ya tabbatar da mutuwar Hausawa 10.
"A halin da ake ciki akwai gawar mutum bakwai Hausawa da aka kawo ofishin 'yan sanda, sai kuma mutum biyu da ke wani gida da ba a ɗauko gawarwakinsu ba. Kazalika yanzu aka zo min da bayanin cewa akwai gawar wani Bahaushe da aka gano yashe a kan titi," in ji shi.
"An kwantar da 'yan uwanmu Hausawa fiye da 100 a asibitoci daban-daban yayin da ɗaruruwa ke neman mafaka a wuraren 'yan uwa, wasu kuma sun gudu Legas, wasu ma sun koma Arewa. Lamarin ya yi matuƙar muni."
Amma Rabi'u, ɗaya daga cikin mutanen da ke neman mafaka a gidan Sarkin Hausawan Shasha, Malam Haruna Mai Yasin, ya shaida wa BBC Hausa cewa an kashe Hausawa kusan 20 a rikicin.
Ya ƙara da cewa bayan aukuwar lamarin na kasuwar Shasha a ranar Alhamis da yamma, 'yan bangar Yarabawa sun samu labarin cewa Bahaushe ya kashe ɗan uwansu shi ya sa suka "riƙa shiga gida-gida inda Hausawa suke da zama suna kai musu hari".
"Mutanen rike da bindigogin da aka yi da ɗan boris sun fito daga yankuna irin su Bodija, Mokola duka a Ƙaramar Hukumar Akinyele, sun ƙone shaguna sama da 250 a kasuwar Shasha, wasu ma na 'yan uwansu ne Yarabawa. Kazalika sun riƙa tare hanya suna kashe Hausawa," in ji shi.
Rabi'u ya ce abokansa biyu 'yan asalin Jihar Kano da Sokoto suna cikin waɗanda aka kashe abin da ya sa shi da wasu mutane suka ruga gidan Sarkin Shasha domin neman mafaka.
Ya ƙara da cewa: "Wallahi mu nan da ke gidan Sarki mun kusa 400. Muna tsoron kar a kashe mu, shi ya sa muka gudo nan domin tun da lamarin ya faru hukumomin tsaro ba su ɗauki matakin da ya dace ba".
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce a iya saninta mutum ɗaya ne ya mutu a hatsaniyar.
Kakakin rundunar, Olugbenga Fadeyi, ya shaida wa BBC Hausa cewa "duk wanda ya ce muku fiye da mutum guda ya mutu ƙarya yake".











