Aung San Suu Kyi : Sojojin da suka hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan kisan Musulmai sun naɗa ministoci

Wani gidan talabijin da ke karkashin ikon soja a Myanmar ya sanar da nadin sabbin ministoci domin maye gurbin waɗanda aka kora daga mulki bayan kifar da gwamnati a ranar Litinin.

Jam'iyyar shugaba Aung San Suu Kyi da ta yi nasara a zaben watan Nuwamban da ya gabata ta National League for Democracy ta yi kira da a gaggauta sakinta.

An tsare Suu Kyi ne fiye da kwana guda bayan sojoji a Myanmar sun yi juyin mulki tare da tsare manyan zababbun 'yan siyasa.

Tuni sojojin suka sake buɗe birni na biyu mafi girma a ƙasar na Yangon bayan rufe shi a jiya, da kuma katse sadarwar Internet.

Sojoji na kan titunan birnin, da ma a babban birnin kasar Naypyidaw, yayin da suke kara shirin ci gaba da kasance a kan mulki.

Yadda ta hau mulki

Aung San Suu Kyi ta kwashe kusan shekara 15 a tsare tsakanin 1989 zuwa 2010.

A 1991, an ba ta lambar yabo ta Nobel Prize yayin da take tsare a gida kuma an yabe ta a matsayin "mai jajircewa duk da rashin ƙarfin ikonta".

Gwamnatin Obama ta cire takunkumin da ke kan Myanmar bayan da suka koma Dimokuraɗiyya

Gwagwarmayarta ta kawo dimokuraɗiyya mulkin soja na wancan lokaci a Myanmar ya sa ta zama wata alama ta son zaman lafiya duk da zaluncin da ke gudana a ƙasar.

A watan Nuwambar 2015 ne ta jagoranci jam'iyyar NKD ta yi nasara a zaɓen dimokuraɗiyya na farko cikin shekara 25.

Kundin tsarin mulkin Myanmar ya haramta mata zama shugaba saboda tana da ƴaƴa da ba ƴan ƙasar ba.

An hamɓarar da shugabar Myanmar da ta goyi bayan yi wa Musulmai kisan kiyashi

Mutumin da ya maka Aung San Suu Kyi gaban kotun duniya

Amma duk da haka ana yi wa Suu Kyi, mai shekara 75 a yanzu kallon shugabar ƙasar mai cikakken iko.

A hukumance ana kiranta 'state counsellor" wato mai bai wa gwamnati shawara. Shugaban ƙasar, Win Myint, na hannun damanta ne.