Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aung San Suu Kyi: Sojojin Myanmar sun hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan yi wa Musulman Rohingya kisan kiyashi
Sojoji a Myanmar sun kifar da gwamnatin shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi.
Kakakin jam'iyya mai mulki ta National League for Democracy wato (Nasr) ya tabbatar da cewa yanzu haka tsohuwar shugabar na tsare a hannun sojoji, tare da wasu manyan ƴan majalisar zartarwarta.
A halin da ake ciki dai ƙasar na tsaka da fama da tankiya tsakanin gwamnatin farar hula da jagororin soja da ke zargin cewa ana tafiyar da al'amura ba daidai ba.
Hatta a zaɓen watan Nuwamban bara, jam'iyyar shugabar ta samu isassun kujeru domin kafa gwamnati, amma sojoji sun kafe a kan cewa an yi magudi a zaɓen.
An baza sojoji na a kan titunan manyan biranen kasar sanna an takaita hanyoyin sadarwa. Yanzu dai babban jami'i a rundnar sojin kasar shi ne yake jan ragamar mulkinta kuma gidan talbijin na sojin kasar ya sanar da ya sanya dokar ta-baci ta tsawon shekara guda.
Ms Suu Kyi ta yi kira ga magoya bayanta da kada su "amince da wannan" kuma su "bijire wa juyin mulkin".
Har zuwa shakearar 2011 sojoji ne ke mulkin Myanmar, kafin daga bisani farar hula suka karba.
Da ma can Shugaba Suu Kyi ta taɓa kwashe tsawon shekaru a tsare.
Wanne hali ake ciki a yanzu?
Sanarwar rundunar sojin ta ce an miƙa mulki ga babban kwamandan sojin ƙasar mai suna Min Aung Hlaing nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Gidajen rediyo da talabijin na kasar sun kasance a kashe, kuma an katse layukan waya da na intanet.
Ana iya hango sojoji na ta faman sintiri fuskokinsu a murtuƙe a kan titunan babban birnin kasar Naypyitaw da kuma babban birnin Yangon.
Bayanan da muka samu na baya-bayan nan na tabbatar da cewa sojojin da suka yi wannan juyin mulki sun kafa dokar ta ɓaci a sassan ƙasar baki ɗaya.
Kamata ya yi majalisar dokokin ƙasar ta sake zama don tsawaita wa'adin shugabar da aka hambarar, amma yanzu sai dai kawai ace yadda sojojin suka dama haka za a sha.