Musulman Rohingya 14 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

A kalla mutum 14 ne suka nutse a teku bayan da wani jirgin ruwa dauke da Musulman Rohingya 'yan gudun hijira ya kife a kudu da gabar tekun Bangladesh, in ji jami'ai.

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Malaysia ne kuma yana dauke da 'yan gudun hijirar Rohingya daga sansanonin Bangladesh, kamar yadda hukumomin kasar suka shaida wa BBC.

Dukkan gawarwakin da aka samo zuwa yanzu duk mata ne da yara.

Wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kusan mutum 70 aka ceto. Sai dai har yanzu ba a ga wasu da yawa ba.

Jirgin ruwan ya yi hatsarin ne a tekun Bay of Bengal kusa da tsibirin Saint Martin.

A watan Agustan 2017 ne sojojin Myanmar suka yi wa Musulan Rohingya mummunar dirar mikiya inda dubun-dubatar su suka tsallake suka bar kasar zuwa Bangladesh.

Da yawansu suna zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira kuma wasun su sun yi kokarin tserewa zuwa Malaysia.