Za a yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin Najeriya, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya sa hannu kan wasu dokoki biyar da majalisar dokokin jihar ta amince da su.
Daga cikin dokokin, har da dokoki biyu da suka yi tanadin hukunce-hukunce masu tsanani kan aikata laifin satar mutane don neman kudin fansa da kuma laifin fyaɗe.
Ramatu Adamu Gul-ma, kwamishinar shari'a kuma babbar lauyar gwamnatin jihar ta Kebbi, ta shaida wa BBC cewa a baya, ƙarƙashin tsarin dokar Penal Code, laifin da aka yanke wa masu aikata garkuwa da mutane shekara bakwai ne amma a yanzu "an canja an tsananta hukuncin saboda abin da yawaita."
A cewarta, gwamnatin jihar ta amince da dokar yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka samu da aikata fyaɗe saboda yadda matsalar ta fyaɗe take ci gaba da ta'azzara.
Ta ce tsananta dokar zai sa masu sha'awar aikata irin waɗan nan laifuka su fasa ganin yadda laifukan suka ƙaru da kashi 50 cikin 100.
"Da can da wuya ka ji an yi wa mutum fyaɗe, da mutane ai ba su san mene ne garkuwa da mutum ba, ka kama mutum ka wahalar da shi ka ce sai an ba da kaza, toh yanzu ga shi yana yawaituwa". in ji Ramatu Adamu Gul-ma.
Matsalar satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na neman zama wani abu da aka saba da shi.
Amma karuwar fyade za a iya cewa a duk kasar ne, wanda a ganin Rahmatu Gulma da irin wadannan hukunci za a iya kawo karshen matsalolin biyu.












