Amy Coney Barrett: Wace ce matar da Trump ya zaba don zama alkaliyar Kotun Kolin Amurka?

Zabin da shugaba Trump ya yi wa Amy Coney Barrett a matsayin alkaliyar Kotun Koli bai zo da wani mamaki ba.

Shugaba Trump wanda shi ne shugaban Amurka a yanzu ya ce ya jima yana dakon samun damar da zai nada ta a matsayin alkaliyar Kotun Koli idan wani daga cikin alkalan da ke kai musamman masu yawancin shekaru ya mutu.

Cikin kasa da mako guda ne shugaban ya zabo matar mai shekaru 48 a duniya, kana mai tsatstsauran ra'ayi, abin da ke nufin cewa a yanzu ya samu damar karkata kotun ga masu tsatsauran ra'ayi da dama can yawancin alkalanta su ne.

Yayin da Amy ta kasance mai goyon bayan damar da jama'a ke da ita ta mallakar bindiga wacce ta gada wato Beder Ginsburg na sukar damar, sannan kuma tana da tsatstsauran ra'ayi kan abin da ya shafi shigowar baki a cewar Jonathan Turley, na jami'ar George Washington.

Sannan ra'ayinta na sukar damar zubar da ciki da auren jinsi ya sa ta yi shuhura kwarai da aniya kasancewar ta zurfafa a kan addini, abin da yasa yawancin 'yan Democrat ke sukar ta.

Sannan kuri'arta a yanzu, za ta bada damar yin sauye-sauye da dama musamman kan abin da ya shafi dokar zubar da ciki da shirin inshorar lafiya na Obama Care da shugaba Trump ke son sokewa.

Sai dai a matsayinta na mai ra'ayin addini sosai ta sha nanata cewa ra'ayinta bazai shafi aikinta ba.

Barrett na zaune ne a Kudancin jihar Indiana, tare da mijinta, Jesse, wani tsohon mai gabatar da kara na tarayya wanda yanzu yake tare da wani kamfani mai zaman kansa, sannan ma'auratan suna da yara bakwai.

An san ta da kaifin basira, ta yi karatu a Jami'ar Notre Dame, ta kammala karatun farko a ajin ta, kuma ta kasance mataimakiya ga Mai Shari'a Antonin Scalia, wanda, a ta bakin ta, shi ne "tsayayyen mai ra'ayin mazan jiya" a Kotun Koli a lokaci.

Kamar wanda take koyi da shi wato Scalia, ita ma tana goyon bayan fassara kundin tsarin mulki dai-dai da yadda marubutansa suka rubuta shi tun fil azal.

Sai dai masu sassaucin ra'ayi da dama na ganin hakan kuskure ne, musamman la'akari da yadda zamani ke yawan canjawa.

Ta shafe tsawon shekaru a matsayin Farfesa a jami'ar Notre Dame, in da taɓa lashe lambar Farfesa mafi kwarewa a shekaru daban-daban.

Wani abokin karatunta Deion Kathawa ya shaidawa BBC cewa ta yi suna ne saboda yadda take ba wa kowa damar tofa albarkacin bakinsa a yayin tattaunawa, ''tana da adalci, sannan tana da hazaka'' a cewarsa.

Shugaba Donald Trump ya zabe ta a matsayin alkaliyar kotun daukaka kara a shekarar 2017, kuma tana aiki da rukunin alkalai bakwai a Chicago.

Jaridar South Bend Tribune ta taba yin hira da wani abokinta, da ya ce tana tashi tun kusan karfe hudu zuwa biyar na safe, abin da wani farfesa a jami'ar da ta yi karatu wato Paolo Carozza ya gaskata.

Carozza ya ce a gabansa Barrett ta samu ci gaba tun daga daliba zuwa malama zuwa alkaliya, ''don haka na santa sosai'' in ji shi.

Ana kyautata zaton za a samu gagarumar muhawara yayin tabbatar da ita, domin sanatoci kamar Dianne Feinstein na da ra'ayin cewa ko tantama babu tsatstsauran ra'ayin addininta zai shafi aikinta.

Barrett ta sha kare kanta a lokuta da dama ''Zan fada muku cewa ra'ayin addinina ba zai shafi aiki na ba a matsayina na alkaliya''.

To sai dai alakarta da wata kungiyar kiristoci ta Peoples of Praise na janyo cece-kuce musamman kan yadda kungiyar ke sukar auren jinsi.

Kungiyoyin masu kare auren jinsi a kasar sun soki zabin na shugaba Trump, suna bayyana ta a matsayin babbar barazana ga auren jinsi.

Ana ganin cewa zazzafar muhawarar da za a samu yayin tabbatar da ita na iya karkatar da hankalin al'ummar kasar daga kan yakin neman zabe.