Dajin Falgore: Yadda masu garkuwa da mutane ke damun mazauna yankin

..

Rundunar 'yan sanda jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a dajin Falgore.

Sannan rundunar 'yan sandan ta ce ta sami nasarar gano bindigogi guda uku a cikin dajin amma ba ta kai ga kama masu aikata wannan laifi ba.

Tun gabanin yunƙurin rundunar 'yan sandan, al'ummar yankin dajin Falgore da ke ƙaramar hukumar Doguwa a kudancin jihar sun ce a baya-bayan nan masu garkuwa da mutane sun matsa wa hanyar da ƙauyukan da ke dajin.

Wani ganau a yayin wani hari da aka kai na baya-bayan nan ya ce suna cikin wani hali na zaman fargaba sakamakon yadda a cikin mako biyu aka yi garkuwa da mutane sama da 30.

Ya ce ko a jiya Litinin sai da masu garkuwa da mutanen suka tare hanyar zuwa garin Doguwa daga Kano a dajin Falgoren suka tafi da mutane tare da raunata wasu.

"A gaskiya ɓarayin na takurawa mutane don nema ma suke su kashe hanyar baki ɗaya, don lokaci zuwa lokacin suke tare hanyar su kama mutane, sai su nemi a ba su kuɗade, a cikin kusan mako biyu masu satar mutanen sun yi garkuwa da mutum a kalla 30''.

''Sannan ko a jiya sai da suka tare hanyar suka tafi da mutane, bayan da suka haɗa su da wasu daga cikin mutanen suka kai su cikin dajin na Falgore, shi ne wasu daga cikin waɗanda aka sace ɗin suka yi amfani da wannan dama suka gudu inda su kuma masu garkuwa da mutanen babu bindiga a hannunsu, sai adda da sanduna sai suka sassari wasu daga cikin mutanen", in ji mutumin.

To sai dai a cewar runudunar 'yan sandan Kano, ta bakin kakakinta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce tana da masaniyar abin da ke faruwa a dajin na Falgore.

Ya ce wa BBC: "Bayan mun samu labarin abin da ke faruwa sai Kwamishina Habu A Sani ya tura rundunar 'yan sanda ta Puff Adar, inda suka je suka sami nasarar ceto mutum biyar sannan suka miƙa wasu da suka samu raunuka asibiti don a duba lafiyarsu sakamakon sara da suka samu daga masu garkuwa da mutanen" in ji DSP Kiyawa.

Sannan ya ce duk da haka akwai jami'ansu da suka bazu a cikin dajin don ci gaba da sintiri don tabbatar da tsaro a dajin da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da shi.

To sai dai masu sharhi kan al'amarun yau da kullum na ci gaba da dasa ayar tambaya kan yadda har yanzu ake ci gaba da samun ɓullar masu garkuwa da mutane a dajin na Falgore, duk da samar da sansanin sojoji da na 'yan sanda a cikin dajin da gwamnatin jihar Kano ke ikirarin ta yi.

Haka zalika ko a shekarun baya sai da gwamnatin Kano ta samar da hukuncin kisa ga dukkan wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a faɗin jihar, wanda ake kallon ya yi tasiri wajen raguwar matsalar.

Abin jira dai a gani a yanzu shi ne ko wane mataki mahukunta a jihar za su ɗauka kan wannan batu? Lokaci ne kaɗai zai iya tabbatar da hakan.