Messi 'zai koma New York City FC, an gindaya wa Barcelona sharaɗin rabuwa da Suarez'

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta shirya biyan dan wasan Barcelona da Argentina mai shekara 33 Lionel Messi £450m a wani bangare na shirinta na shekara biyar wanda daga karshe zai kai shi ga tafiya New York City FC, in ji jaridar (Sport, via Daily Star)
Dole Barcelona ta biya £12m idan tana so ta soke kwangilar dan wasan Uruguay mai shekara 33 Luis Suarez'. (Goal)
Jaridar Mirror ta rawaito cewa Tottenham ta yi yunkurin yin katsalandan a shirin Manchester United na dauko dan wasan Netherlands and Ajax Donny van de Beek, mai shekara 23.
Manchester United ta tattauna da Aston Villa a yayin da take son cimma matsaya don karbo dan wasan Ingila mai shekara 24 Jack Grealish. (Mail)
Manchester United ta bi sahun Liverpool a fafutukar dauko dan wasan Bayern Munich da Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (Dagbladet TV, via Sun)
Kazalika Leeds United na son dauko dan wasan Udinese da Argentina Rodrigo de Paul sai dai an gaya mata farashin dan wasan mai shekara 26 ya kai £31m. (Guardian)
Tottenham da Newcastle na son dauko dan wasan Bournemouth da Norway Josh King, mai shekara 28. (Chronicle)
Valencia ta nemi dauko dan wasan Arsenal da Faransa mai shekara 21 Matteo Guendouzi. (Super Deporte - in Spanish)
Dan wasan Barcelona da Chile Arturo Vidal, mai shekara 33, zai iya komawa tsohuwar kungiyarsa Juventus. (Goal)
Kocin Inter Milan Antonio Conte yana son dauko dan wasan Faransa N'Golo Kante, mai shekara 29, daga Chelsea. (Football Italia)
Dan wasan West Ham da Faransa l Sebastien Haller, mai shekara 26, ya ki amincewa da tayin tafiya Hertha BSC. (90 mins)











