Mutuwar Isma'ila Isa Funtua ta bar babban giɓi – Shugaba Buhari

Mamman Daura tare da Marigayi Isma'ila Isa Funtua

Asalin hoton, Twitter/@ibrahimado__

Bayanan hoto, Mamman Daura tare da Marigayi Isma'ila Isa Funtua

An yi jana'izar Malam Isma'ila Isa Funtua jana'izar aboki kuma makusancin Shugaba Muhammadu Buhari a Masallacin Shehu Shagari da ke Area 1 a Abuja, babban birnin kasar.

An yi jana'izar ne ta hanyar bin dokokin nesa-nesa da juna don hana yaduwar cutar korona.

Manyan jami'an gwamnati da manyan mutane da dama ne suka halarci jana'izar. Tuni dai aka binne shi a makabarar Gudu da ke birnin.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar amininsa Malam Isma'ila Isa Funtua wanda ya rasu ranar Litinin.

Shugaban ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai da 'yan uwa da kuma al'ummar Jihar Katsina da ma sauran makusantan marigayin bisa rasuwarsa.

Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin "mutum na kowa da ake matuƙar girmamawa."

Fadar shugaban ba ta yi wani cikakken bayani ba game da dalilin rasuwarsa amma an ruwaito makusantansa na cewa ya rasu ne sanadiyar bugun zuciya.

Malam Isma'ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin suna da tasiri a gwamnatin Buhari.

Kuma tsakanin wata uku dai yanzu shugaban ya rasa manyan aminansa guda biyu bayan rasuwar Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadarsa da ya rasu watan Afrilu.

Shugaba Buhari ya ce rasuwarsa ta haifar da babban giɓi ne kasancewar ya taimaka masa musamman a tafiyarsa ta siyasa.

Ya kuma yi addu'ar Allah Ya ji ƙan Malam Funtua, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure rashinsa.

Rasuwar Malam Sama'ila Funtua

Malam Sama'ila Funtua ya rasu ne sakamakon bugun zuciya ranar Litinin, a cewar ɗaya daga cikin 'yan uwansa.

"Mallam ya faɗawa iyalinsa cewa yana son ganin likita amma sai da ya fara zuwa wajen mai aski. Daga nan kuma ya tuƙa mota zuwa asibiti," in ji ɗan uwansa wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa.

Isma'ila Isa Funtua ɗan kasuwa ne kuma jami'in gwamnati da ke da ƙwarewa sama da shekara 30.

Marigayin ya taba rike muƙamin minista sannan ya taba jagorantar kungiyar masu buga jarida ta NPAN na tsawon shekara takwas.

Shi ne ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin ƙere-ƙere da ya gina muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya.

Alhaji Isma'ila Funtua ne kuma daraktan gudanarwa na farko na jaridar Democrat.