Tolulope Arotile: Abubuwa 10 kan ƴar Najeriyar da ta fara tuƙa helikwaftan yaƙi

Asalin hoton, NIGERIAN AIR FORCE HQ/FACEBOOK
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile sakamakon hatsarin mota a Kaduna.
Ga abubuwa 10 da kuke bukatar sani kan ƴar Najeriyar da ta fara tuƙa helikwaftan yaƙi wacce ta mutu a ranar Talata 14 ga watan Yulin 2020.
Tolulope Arotile 'yar asalin Ƙaramar Hukumar Ijumu ce da ke Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya.
Ta girma ne a Jihar Kaduna, inda ta fara karatun firamarenta a makarantar sojojin sama ta Nigeria Airforce Primary sannan ta halarci sakandaren Airforce.
Hakan ya ba ta damar share wa kanta hanyar shiga aikin soja tun tana 'yar ƙaramarta.
Babu jimawa ta gama samun horo na musamman a cibiyar Starlite International Training Academy a Afirka Ta Kudu, kuma ta samu kyakkyawan sakamako.
Kazalika ita ce ɗaliba mafi hazaƙa lokacin da ta kammala karatu a rundunar Sojan Sama ta Najeriya a shekarar 2017.


A watan Satumban shekarar 2017 ne aka gabatar da Tolulope a matsayin mace ta farko mai tuƙa jirgin yaƙi tare da Kafayat Sanni.
An kaddamar da ita ne bayan da ta kammala kwasa-kwasanta na koyon tukin jirgin sama a Amurka da Afirka Ta Kudu.
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Mashal Sadiq Abubakar ya kira Tolulope da suna "Matukiyar ta musamman" a wani jawabi da ya gabatar a yayin kaddamar da ita wanda aka yi a Abuja.
Sadik Abubakar tare da Ministar Mata ta Najeriya Dame Paulline Tallen ne suka sa wa Tolulope aninin karin girma
A cewar rundunar sojin Najeriya, ta taimaka kwarai wajen yaki da 'yan bindiga a jihohin tsakiyar kasar ta hanyar kai musu hare-hare ta sama a wani shirin na GAMA AIKI a Minna na jihar Naija.
Tolulope Arotile ba ta yi aure ba gabanin mutuwarta a ranar 14 ga watan Yulin 2020.
Ta mutu tana da shekara 22 a duniya.












