Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar fyade: Abu biyar da suka kamata ku sani kan fyade a Kano
Matsalar fyade ta jima tana ciwa al'umma tuwo a kwarya musamman a Najeriya. A baya-bayan nan dai, hankulan al'ummar Najeriya sun yi matuƙar tashi sakamakon ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu.
Fyade bai tsaya a kan manya ba ko 'yan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.
A kan haka ne BBC ke ta wallafa wannan labarin domin sanar da al'umma abu biyar da ya kamata kowa ya sani kan fyaɗe domin ya zama kandagarki musamman ga mata da kananan yara waɗanda ba su da karfi kare kansu.
1 - Yawancin wadanda aka yi wa fyade sun san wanda ya aikata fyaden a kansu.
- Kashi 33.3 cikin 100 wato ɗaya cikin uku na illahirin laifukan fyaɗe, a cikin kangwaye gidaje ake aikata su.
- Kashi 20.8 cikin 100 ana aikata su ne a gonaki da burtalai, yayin da kashi 16.7 cikin 100 na fyaɗe a gidan waɗanda aka yi wa cin zarafin ake aikata su.
- Sannan kashi 10.4 cikin 100 na fyaden da aka aikata a gidan shi mai aikata laifin ake yin sa.
2 - A yawan lokuta kananan yara aka fi yi wa fyade
Sama da kashi 40 na waɗanda ake yi wa fyaɗe, bayan an yaudare su da kuɗi ko abinci ne ake aikata laifin."
A ko da yaushe ana shawartar mazauna unguwanni da suka ƙara sanya ido a kan take-take da kai-komon mutane a yankunan, da nufin kare 'ya'yansu da kuma iyalansu.
3 - An fi aikata fyade a wasu ranakun mako da lokutan yini
Binciken ƴan sanda ya kai suna bibiyar waɗanne ranaku ne da awoyin aka fi yin aikata laifuka na fyaɗe.
Wannan ke nan na nufin ya kamata iyaye su kula da wuraren da ƴaƴansu suke a ko wane lokaci domin kare su daga faɗawa cikin hatsari.
4 - Yawancin mutane ba sa fitowa fili su sanar da hukuma bayan an aikata fyade
Wannan kuskure ne, domin a dalilin haka ake karfafa wa masu yi fyade su ci gaba da aikata ta'asar da suke yi.
Idan ana fitowa fili ana sanar da hukuma, za a sauya al'amura, domin hukuncin da ake yanke wa masu fyade zai hana wasu masu sha'awar aikata laifin afka wa kan wasu.
Sannan al'umma za ta fahimci girman matsalar har ma ta kyamaci masu aikata fyade a maimakon yadda ake rufa-rufa kan matsalar.
Daga farko shekarar 2020 zuwa watan Yuni, ƴan sandan jihar Kano sun karɓi ƙorafe-ƙorafe kan aikata fyaɗe guda 45.
5 - Masu aikata fyade ba sa la'akari da yawan shekarun wadanda suka yi wa fyade ko irin tufafin da suka sanya
Wannan ne ya sa ake samun an yi wa ƙananan yara har da matan da suka tsufa fyade.
Fyade ba laifin wadanda aka afka mu su ne ba.
Abin lura a nan shi ne a duk lokacin da aka taras da wani ya afka wa wata ba tare da amincewarta ba, to fyade aka aikata.
Ko a makon jiya sai da rundunar 'yan sandan Kano ta gurfanar da wani mutum gaban kotu bisa zargin yi wa mata kusan 40 fyade, ciki har da wata mai shekara 80 da haihuwa.
Akwai kuma rahotanni da ake samu na yadda aka yi wa jarirai da kanan yara fyade.
Me ke janyo fyaɗe?
Tsananin bukatar yin jima'i - Likitoci sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.
Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.
"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyaɗe suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato wata jarabar matuƙar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."
Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a riƙa yi musu magani tare da da ba su shawarwari.
Taɓin ƙwaƙwalwa - Dr Shehu Saleh shugaban asibitin kula da masu lalular ƙwaƙwala da ke garin Kware a jihar sokoto ya ce matsalar taɓin ƙwaƙwalwa na daga cikin dalilan da ke sa wasu su aikata fyaɗe musamman wadanda ba za su iya bambance abu mai kyau da marar kyau ba, kamar waɗanda ke aikata sata ko fashi da makami.
"Duk za su iya aikata fyaɗe saboda ba su san cewa laifi ne suka aikata ba, saboda ƙwaƙwalwarsu ta juye."
Sai dai Likitan ya ce yawancin masu aikata fyaɗe dama ce suka samu tsakaninsu da waɗanda suke yi wa fyaɗen da kuma mugun halin da ke ransu.
Ya ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi ya biya bukatarsa ta samun gamsuwa amma saboda mugun halin da ke ransu ke sa su aikata yin fyaɗe.
Likitan ya ce fyaɗe na iya jefa yaran da aka yi wa cikin damuwa kan mugun abin da aka aikata masu, wanda zai iya shafar ƙwaƙwalwarsu.
"Babban matsalar fyade shi ne yaran da aka yi wa fyaden, yana janyo masu taɓin hankali har ta kai su ma suna yi wa wasu fyaden," in shi Dr Shehu Saleh.
'Tsattsauran hukunci'
Wasu dai na ganin rashin hukunta wadanda aka samu da laifin fyaɗe ne yake sanya al'amarin yake kara ta'azzara.
Uwar gidan shugaban Naijeriya, Aisha Buhari, ta taba bayyana damuwa game yadda ake sassauta wa masu yi wa mata fyade a Najeriya, tana mai kira da a tsaurara dokokin hukunta wadanda aka samu da laifin.
Aisha Buhari ta yi kiran ne a watan Disamban 2017 bayan wata shari'ar da aka yi a jihar Kano inda aka ci wani mutum tarar naira dubu goma kacal bayan an same shi da laifin yi wa wata jaririya fyade.
Uwar gidan shugaba kasar dai tana son a gyara dokokin ƙasar ta yadda duk wanda aka samu da laifin cin zarafin mata da kananan yara ba zai sake yin lafin ba.
Kungiyoyi masu zaman kansu dai na dora alhakin habakar matsalar akan rashin doka mai karfi na hukunta wadanda ke aikata laifin fyade a Najeriya.
Malaman addini a nasu ɓangaren na ganin ana samun yawaitar fyaɗe musammam a kan kananan yara ne saboda neman abin duniya.
Dr Abdullahi Pakistan, wani Malamin addinin musulunci a birnin Kano ya ce abu uku ne ke haddasa wannan matsala:
"Tsananin neman duniya, inda za ka ga boka ko matsafi ya bukaci mutum ya aikata fyade ko ya cire agarar wani, ko kuma ya tono gawa domin biyan bukatunsa.
Sai kuma shaye-shaye da ke batar da hanakalin mutane ta yadda ba sa sanin abin da suke aikatawa, da kuma tasowa cikin rashin tarbiyya.
"Mutane ba su san abin da ake kira tausayi ba. Duk mutumin da bai samu tausayi ba, ba zai tausayawa wani ba," a cewar babban malamin Islamar.
Malamin ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su rika yanke tsattsauran hukuncin kan duk mutumin da aka samu da laifin fyaɗe, sannan a gefe ɗaya kuma iyaye su duƙufa wajen yi wa ƴaƴansu tarbiyya baya ga wa'azi da Malamai za su mayar da hankali wajen yi wa al'umma kan illar wannan matsala.
Da alama dai wannan batu zai ci gaba da jan hankalin mutane a Najeriya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga ƴan ƙasar da ma hukumomi, wadanda ake buƙatar su ɗauki matakai ƙwarara domin shawo kansa.
Tsoron tsangwamna
Galibi ana ganin rashin fitowa a kai kuka ga hukumomi da kuma karancin hukunci mai tsanani a kan fyade ne ke taimakawa aukuwar matsalar.
Masana suna alakanta rashin fallasa zancen fyade ga dalilai na addini da al'ada da kuma rashin son kunyata a cikin al'umma.
Sau da yawa a kan samu iyaye maza da suke yi wa ƴaƴansu ƴan mata fyade amma saboda gudun abin kunya, sai a lullube maganar.
A mafi yawancin lokaci, da zarar an ɗaga irin wannan maganar, abin da ke biyo baya shi ne kyama daga wurin al'umma.
A wani lokaci a akan samu yanayin da yarinya ba za ta samu manemi ba sakamakon fuskantar matsalar fyade duk kuwa da cewa ba a son ranta aka yi mata fyaden ba.
Wasu na ganin girman matsalar fyaɗe da illolinsa ga makomar mace ya kai girman da ya kamata duk wadda aka yi wa ta fito ta bayyana domin hukunta waɗanda suka aikata mummunan laifin wanda shi zai kawo ƙarshen matsalar.
Sannan zartar da hukunci mai tsauri zai zama izina ga masu aikata fyaɗe.
Mene ne fyade?
Dakta Nu'uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma a cewarsa, "fyaɗe yana nufin haike wa mata, wani sa'in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba."
Dakta Nu'uman ya ce tasirin fyaɗe na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan daɗe a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.
"Duk wanda suka haɗu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar takan daɗe tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce", a cewarsa.
Sai dai bisa alama jama'a ba su gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da suka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace.
Idan aka yi wa wata ko wani fyaɗe, shi da iyalansa sukan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙyama da ake nuna wa waɗanda aka yi wa fyaɗe da iyalansu.
Kuma wannan yana hana jami'an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.
Abin da ya fi dacewa
Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke ayyukan kula da mata da kananan yara da marayu a jihar Kaduna a Najeriya, mai suna ARRADA ta shawarci jama'a musamman iyaye kan yadda ya kamata su kula da kai komon 'ya'yansu.
- Ya kamata iyaye musamman mata su sanya ido kan masu kula da ƴaƴansu, misali direba ko kuma mai aiki.
- Iyaye su kula sosai da mutanen da ƴaƴansu suke matuƙar shakuwa da su misali kawunni ko gwaggo ko anti da dai sauransu.
- Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko kuma ba su kyaututtuka.
- Ka da iyaye su rinka korar ƴaƴaansu da su je su yi wasa domin ƙyale su don su shakata.
- Iyaye mata su rinka duba al'aurar yaƴansu musamman idan suka zo suna kuka saboda ba su san komi ba.