Liverpool ta so dauko Odegaard, West Ham da Crystal Palace na zawarcin Maja

Josh Maja

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta yi yunkurin sayo dan wasan Norway mai shekara 21 Martin Odegaard a bazarar da ta wuce, kafin Real Sociedad ta yi aronsa daga Real Madrid, a cewar tsohon kocinsa Leonid Slutsky. (Metro)

West Ham da Crystal Palace na sha'awar sayo tsohon dan wasan Sunderland Josh Maja, mai shekara 21, a yayin da dan wasan na Najeriya yake son komawa Ingila daga Bordeaux a bazara. (Sun on Sunday)

Tsohon dan wasan Najeriya Abdul Sule ya ce wata kungiyar da ke buga gasa a Turai na iya kwace Odion Ighalo, mai shekara 30, daga Manchester United idan bata saye shi daga Shanghai Shenhua a bazarar nan ba. (Goal)

Wakilin James Rodriguez ya tattauna da Manchester United da Juventus da zummar yiwuwar komawar dan wasan na Colombia daga cikinsu daga Real Madrid. (AS)

Zakarurancin da Nemanja Matic yake nunawa ya sa Manchester United bata da zabin da ya fi mata sabunta kwantaragin dan wasan na Serbia mai shekara 31. (Mail)

Coventry City na fatan sabunta kwantaragin dan wasan Ingila mai shekara 23 Zain Westbrooke, wanda ake rade radin zai koma Derby County.(Derby Telegraph)

An doke Liverpool a cinikin dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20, lamarin da a yanzu ya mayar da Manchester United a gaba-gaba wajen yunkurin sayen dan wasan da aka sanya wa farashin da ya kai £88m. (Football Insider)

Kungiyoyin Gasar Firimiya da ke son dauko dan wasan RB Leipzig mai shekara 21 Dayot Upamecano - wadanda suka hada da Arsenal, Tottenham da kuma Manchester City - sun samu koma-baya, yayin da Real Madrid ta shirya tsaf don dauko dan wasan wanda ke buga wa Faransa gasar Under-21. (Sunday Mirror)