Coronavirus ta kashe mahaifiyar Pep Guardiola

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Mahaifiyar Pep Guardiola, Dolors Sala Carrio mai shekara 82 ta mutu a Barcelona, bayan da ta kamu da coronavirus.

Dukkan masu hulda da Manchester City, sun mika ta'aziyya ga Pep Guardiola da iyalansa da dukkan aminansa.

Ranar Litinin mutum 637 suka mutu kuma kawo yanzu jumulla mutum 13,055 suka rasa ransu sakamakon coronavirus a Spaniya.

A makon jiya ne Guardiola ya bayar da gudunmuwar fam 920,000 domin yakar coronavirus.

Ya bayar da kudin ne don sayen magunguna da kayayyakin da za su taimaka wa wadanda ke kula da marasa lafiya da suka kamu da annobar.

Barcelona tana birnin Catalonia daya daga cikin biranen da aka fi kamuwa da coronavirus a Spaniya.

Guardiola, mai shekara 49, ya fara jan ragamar Manchester City a Yulin 2016, bayan da ya horar da Barcelona da Bayern Munich.