Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta sa dokar hana fita

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sa dokar hana fita wadda ke fara aiki daga daren Alhamis a yunkurinta na dakile yiwuwar baza cutar koronabairus a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe ce ta sanar da matakin a wani jawabi da ta yi wa al'ummar jihar.

Ta ce gwamnatin ta dauki matakin ne bayan shawarwarin da wani kwamiti da ke karkashinta mai sa ido kan cutar covid-19 ya bayar duk da yake zuwa yanzu jihar ba ta samu bullar cutar ba.

Matakin na gwamnatin Kaduna na nufin jama'a za su zauna a gidajensu sannan za a rufe wuraren ibada da shaguna da wuraren bukukuwa da kasuwanni.

Haka zalika, gwamnatin ta ce ta haramta bukukuwan aure da sauran tarukan jama'a.

"Gwamnatin Kaduna ba ta da isassun asibitoci da za su kula da wadanda suka kamu da cutar idan ta shiga jihar.

Kalubalen da sauran kasashe masu ingantattun tsare-tsaren kula da lafiya ke fuskanta sakamakon wannan annoba, babban darasi ne ga duk wanda yake shashantar da hatsarin da ake ciki na coronavirus.

"Muna kokari ne na sauke nauyin da ke wuyanmu, na sanar da mutane halin da ake ciki duk da yake ba zai yi wa kowa dadi ba.

Zai fi sauki a kare bullar wannan annoba maimakon a kula da marasa lafiyar da suka kamu da ita da kuma mace-macen da ake iya samu."

A cewarta, an bai wa hukumomin tsaro umarnin kamawa da tsarewa tare da tuhumar duk wanda aka samu da take dokar. Sannan za a rufe masallatai da majami'u - mutane za su rika gudanar da harkokinsu na ibada a gidajensu.

Mataimakiyar gwamnan ta Kaduna ta bayyana cewa za a dauki matakin kwace filayen wuraren gudanar da taruka da ibada, matukar suka keta wannan umarni.

Zamfara ta rufe iyakokinta

Ita ma gwamnatin Zamfara ta sanar da daukar matakin rufe iyakokinta - ba shiga ba fita domin hana bazuwar cutar zuwa jihar.

A cewar wani sako da Gwamnan jihar Bello Matawalle ya wallafa a shafinsa na Tiwita, matakin zai fara aiki ne daga ranar Asabar 28 ga watan nan.