Somalia: An ayyana dokar ta-baci kan farin dango

Farin dango

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Farin dango kan ci abincin da ya kai nauyinsu a kowacce rana, sannan su na lalata amfanin gona

Somalia ta zama kasa ta farko a yankin Sahel da ta ayyana dokar ta-baci kan farin dango da suka addabi kasar tare da lalata amfanin gona.

Ana fargabar cewa ba za a iya shawo kan wadannan fari ba gabanin soma girbin amfanin gona a watan Afrilu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce farin dangon su ne mafi yawan da aka taba samu cikin shekara 25 a kasashen Somaliya da Habasha. Hukumar bunkasa abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita ma makwabciyar Somaliya, wato Kenya ba ta fuskanci barazanar farin dango mai tsanani kamar wannan ba a shekara 70.

Wani manomi a arewa maso gabashin Kenya, Ali Bila WaK'o ya ce lamarin na zuwa ne bayan sun shafe tsawon shekaru suna fama da fari, inda ya ce "akwai ban takaici! Yayin da muke murna mun yi sa'ar dacewa da ruwan sama, sai kuma wadannan kwari suka zo suna lalata mana amfanin gona.

Mun dibga asara saboda kwarin sun cinye min duk waken da na shuka. Yanzu dubi yadda suka lalata min masara. Kuma ba za mu iya amfani da sauran da suka rage ba, don ba mu da tabbacin cewa farin ba sa dauke da guba.''

Somaliya ce dai kasa ta farko a yankin da ta ayyana dokar ta-baci kan wannan annoba, tabarbarewar tsaro kuma a kasar ta sa da wuya a iya amfani da jiragen sama wajen yin feshin magani.

A watan jiya ne, Hukumar bunkasa abinci ta Duniya ta bukaci kai wa Somaliya dauki don yaki da mamayar farin dango a yankin kusurwar Afirka, inda ta yi gargadin cewa adadin fari na iya ninkawa har sau 500 zuwa watan Yuni a fadin yankin.

Farin sun fantsamo ne zuwa gabashin Afirka daga Yemen bayan mamakon ruwan sama a karshen damunar bara. Fara tana iya yin tafiya mai nisan fiye da tsawon kilomita 150 cikin kwana guda.

Kuma idan ta rika tana iya cin abincin da ya kai nauyinta a kullum. A watan Disambar bara, sai da farin dango suka tunkude wani jirgin saman fasinja na kamfanin jirgin Ethiopia. Kwarin sun fantsama injinan jirgin da gilasan gaba da kuma hancinsa, ko da yake dai ya iya sauka lafiya a Addis Ababa, babban birnin kasar.