Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba mu kashe Janar Soleimani don haddasa yaki ba -Trump
Shugaba Trump ya ce kisan da Amurka ta yiwa babban kwamandan Iran Qassem Soleimani ta yi ne da nufin dakatar da yaki ba fara shi ba.
Da wayewar garin Juma'a ne Amurkar ta kai wa kwamandan hari a filin jirgin saman birnin Bagadaza na Iraqi.
A wani jawabi da ya gabatar a tashar talabijin, Mr Trump ya ce Amurka ta yi nasarar kashe dan ta'adda lamba daya a duniya.
A cewarsa Janar Soleimani ya sha kitsa hare haren ta'addanci irin wadanda ya sha kitsawa shekaru 20 da su ka gabata.
To sai dai a nata bangaren Iran ba ta yi wata wata-wata ba wurin sanar da duniya cewa Amurka za ta yi da na sanin aikata abin da ta kira harin ta'addanci, kuma za ta zabi lokacin da take ganin ya dace don mayar da martani.
Babu tantama kisan Janar Soleimani zai kara cakuda zaman da dama na doya da manja ne tsakanin Iran da Amurka kuma zai kara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rashin tabbas.
Haka ma kisan nasa ya haifar da tsadar man fetur a duniya.
Tuni kawayen Amurkar a yankin da suka hada da Saudiyya da Bahrain suka fara kiraye kirayen zaman lafiya.
To sai dai duk da ikirarin mayar da martanin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi da Iran din ta yi, masana na ganin gwamnati a Tehran na da zabin takaita martanin, matsawar ba ta shirya fito na fito ba gadan gadan da Amurka.
Yanzu dai duniya ta zuba ido don ganin ta inda Iran za ta fara, a shirinta na mayar da martani kan kisan babban kwamandanta da a baya shugabannin Amurka da dama suka ji tsoron tabawa.