Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Farashin danyen mai ya tashi a duniya kan kisan Soleimani
Farashin man fetur a duniya ya tashi bayan da Amurka ta kashe babban Janar din kasar Iran.
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun yi gargadin cewa wannan lamarin zai iya kawo fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya kuma zai iya kawo cikas ga samar da man fetur a duniya.
Farashin danyen mai samfarin Brent ya tashi da kusan dala uku inda duk ganga ta koma dala 69.16.
Wannan na zuwa ne bayan wani hari da Amurka ta kai da jirgi mara matuki kuma ya yi sanadiyar kashe Janar Qasem Soleimani a filin jirgin Bagadaza wanda shelkwatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana a matsayin ''matakin kariya''.
Janar Qasem Soleimani, babban soja ne a Iran wanda ya jagoranci dakarun Quds na rundunar juyin juya halin Iran wadda ke aiki a kasashen ketare cikin sirri.
Karuwar farashin man fetur din ya saka farashin hannayen jari sun tashi a Landan inda hannun jarin BP ya karu da kashi 1.5 sai kuma na Dutch Shell da kashi 1.4 cikin 100.
An kwana biyu ana samun fargaba tsakanin Amurka da Iran tun bayan da Amurka ta fita daga wata yarjejeniyar nukiliya.