Shin Sarki Sanusi zai karbi nadin da Ganduje ya yi masa?

Gwamna Ganduje da Sarki Sanunsi

Wannan ita ce tambayar da jama'a da dama na ciki da wajen birnin Kano ke yi dangane da nadin da Gwamna Ganduje ya yi wa Sarki Sanusi a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.

A daren Lahadi ne dai gwamnatin ta jihar Kano a wata sanarwa da babban sakataren hulda da 'yan jaridu na gwamnan, Abba Anwar, ya fitar, ta ce, bisa tanadin sashe na 4 (2) (g) da sashe 5 (1) (2) na dokar masarautun jihar ta 2019, gwamnan jihar ya nada, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, Sarkin Kano a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa daga cikin sauran 'yan majalisar akwai dukkanin sauran sarakunan jihar masu daraja ta daya, na Bichi da Rano da Karaye da Gaya, Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Dr Tafida Abubakar (Autan Bawo), Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa sashe 4 (2) na dokar ya ba wa Sakataren gwamntaiin jihar da kwamishinan kananan hukumomi da shugabanin kananan hukumomi dai-dai daga kowace daya daga cikin masarautun biyar damar zama mambobi.

Akwai kuma akalla masu nada sarki goma, akalla biyu daga kowace masarauta daga cikin su biyar din, haka kuma da babban limamin kowacce daga cikin masarautun.

Nadin ya kuma hada da wasu wakilai na 'yan kasuwa daga masarautun da kuma wakilai na hukumomin tsaro. Sannan kuma shugabancin kamar yadda sanarwar ta bayyana zai zama na karba-karba bayan shekara biyu.

Gaba kura baya sayaki

Mutane da dama, musamman mazauna birnin Kano na yi wa wannan nadi wani kallon wani tarko da gwamnatin Ganduje ta dana wa Sarki Sanusi.

Masu nada sarki tare da masarautar Kano dai sun shigar da kara gaban kuliya inda suke kalubalantar dokar da ta kafa karin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya yi.

Wani masanin tarihi a birnin Kano da bai so a ambaci sunansa ba ya ce "Hakan na nufin idan Sarki Sanusi ya amince da wannan nadin da Gwamna Ganduje ya yi masa to tamkar yana da ja ga shari'ar da ke gaban kotu ne, wato ya amince da sabbin masarautun ke nan."

Ya kara da cewa "ina ganin wata makarkashiya ce gwamnati ta shirya wa mai martaba."

Sai dai mai magana da yawun gwamnati kuma kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ya shaida wa BBC cewa "babu wata makarkashiya da aka shirya wa Sarkin illa dai neman maslaha."

Yanzu dai Sarki Sanusi na da shekaru biyu a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan lokacin da za a juya a bai wa wani sarkin.

'Tarko'

A dokar da Gwamna Ganduje ya rattaba wa hannu ta samar da karin masarautu hudu a jihar a karo na biyu ta kunshi abubuwa da suka hada da hukunta duk sarkin da ya ki halartar zaman majalisar sarakuna sau uku ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Dokar ta ce " Duk sarkin da yaki halartar tarukan majalisar sarakunan har sau uku ba tare da kwakkwaran dalili ba, ya kori kansa daga sarauta."

To sai dai da alama ba abu ne mai yiwuwa ba Sarki Sanusi ya kira wannan taron majalisar sarakunan kasancewar bai ma amince da sarakunan ba.

Wani makusancin fadar Kano wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa "Sarki Sanusi har yanzu bai ma karbi wata takarda daga gwamnatin jiha ba dangane da nadin da gwamnan ya yi masa."

Kamar yadda kowa ya ga wannan sanarwa a shafukan sada zumunta, haka shi ma Sarki ya ga wannan sanarwa."

Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko Sarki Sanusi zai kira wannan taron na majalisar sarakuna da gwamnatin jihar Kano ta nada shi domin jagoranta.