Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karawar karshe tsakanin Dino da Adeyemi
A ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba ne ake gudanar da karashen zabe zagaye na biyu na kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma.
'Yan takarar sun hada da Dino Melaye na jam'iyyar PDP da kuma Smart Adeyemi na jam'iyyar APC.
Bayan zaben da aka gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba (inconclusive.)
A wannan karon za a gudanar da karashen zaben a rumfuna 53.
Ana sa ran cewa masu zabe 45,767 ne za su kada kuri'a daga kananan hukumomi bakwai a fadin jihar.
A zaben da aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar zabe a jihar ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba kasancewar kuri'un da aka soke sunfi yawan wadanda wanda ke kan gaba ya bada tazara.
Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ke kan gaba da kuri'u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam'iyyar PDP ke da kuri'u 59,548.
Hukumar zaben Najeriya INEC a shafinta na twitter ta bayyana cewa tuni aka fara gudanar da zaben a wasu kananan hukumomi a fadin jihar ta Kogi.
A kwanakin baya ne dai kotun sauraron kararrakin zabe ta garin Lokoja da ke jihar Kogi ce ta soke zaben Sanata Dino Melaye, wanda yake wakiltar shiyyar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.