Denmark za ta tallafa wa kasashen yankin Sahel

Yankin Sahel

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar dokokin Denmark ta amincewa gwamnatin kasar da ta taimakawa kasashen yankin Sahel a yakin da su ke yi da 'yan ta'ada.

Daga cikin taimakon da kasar za ta aiko anan gaba wanda zai shiga hannun MISUSMA,ya hada da jirgi da kwararrun ma'aikatan fannoni daban-daban a kalla 75.

A cewar farfesa Addo Mahamane na jami'ar jihar Tawa a jamhuriyar Nijar, kasar Denmark ta lura da irin jajircewa da kasashen suka nuna wurin yakar ta'addanci, don haka ne ta yi tunanin agaza musu.

Ba da jimawa bane kasashen su ka kafa wata gidauniya don tara kudin da za su sayi makaman yakar yan'ta'adda a yankin.

Kungiyar Boko Haram na daga cikin kungiyoyin masu ta da kayar baya da su ka addabin yankin Sahel, musamman a arewacin Nijar.