Darius Isaku: Jukun da Tivi na da damar sasantawa

Gwamnan Taraba a Najeriya ya ce hanyar da ta dace a magance rikicin kabilanci irin na Tivi da Jukunawa da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa a kasar, ita ce ba da damar kafa 'yan sandan jihohi.

Darius Ishaku ya bayyana haka ne bayan kammala wani taron sulhunta rikicin kabilun Tivi da Jukanawa, wanda ya haddasa asarar rayuka da barnata dukiya.

Ko a makon jiya, an kashe wani babban limamin kirista, Rabaran Faza David Tanko a kan hanyarsa ta komawa gida bayan halartar taron sulhunta rikicin a Takun.

Sai dai Group Captain Sadiq Garba mai ritaya, ya ce samar da 'yan sandan jihohi ba shi zai kawo maslaha kan rikicin ba.

Hasalima ya ce daga salon yadda ake tafiyar da lamura a Najeriya, lokaci bai yi ba da za a bai wa jihohi cin gashin kan su na samar da 'yan sandan.

''Saboda idan ka yi duba da yadda tsarin siyasarmu ya ke, wasu za a iya cutar da su ko dai kan banbancin siyasa ko addini ko kabilanci''.

''Babbar matsalar da ake fuskanta a yanzu shi ne, yadda nuna kiyayya ya karu tsakanin al'uma, dan haka dan sanda ba shi zai kawo maslaha tsakanin makofta ba.

Dole su za su sasanta juna, su kauda kiyayya da rashin yadda a tsakaninsu.

Su kuma amince dukkansu dole su mutunta zaman takewar da ke tsakaninin duk da cewa addininsu ba daya ba, kuma al'ada ma haka'', inji Captain Sadiq.

Shekara da shekaru ana fama da rikici tsakanin Jukunawa da kabilar Tivi a jihar Taraba, hakan kuma ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa.