An hana ma'aikatan gwamnati buga waya

Shugaba Macky Sall

Asalin hoton, AFP

A wani yunkuri na rage kashe-kashen kudaden na ma'aikatan gwamnatin Senegal, gwamnatin za ta dakatar da ba da kudin buga waya ga ma'aikatanta.

Ministoci da ma'aikatansu ba za su iya buga waya ba amma za su iya amsar kiran waya daga nan har zuwa karshen Satumba.

Sai dai akwai wadanda matakin ba zai shafa ba kamar jami'an tsaro da ministocin cikin gida.

Gwamnatin Senegal din ta ce za a iya kuma rage wasu kudaden wanda za a yi amfani da su a bangarori na kula da lafiya da ilimi da kuma ayyukan al'umma.

A wani jawabi da ya yi kan sake tsarin ma'aikatun gwamnatin kasar, Shugaba Macky Sall ya ce an kashe dala miliyan 28 a kan sayen waya tun hawan shi karagar mulki a shekarar 2012.

Shugaba Sall ya ce an kashe dala miliyan 518 a kan sayen motoci a shekaru 7 da suka wuce.

A wani yunkuri na sake rage kashe-kashen kudaden gwamnati, an soke wasu mukamai na firaminista da ministocin kasar a farkon shekarar nan.