Zaben Senegal: Macky Sall ya sake zama shugaban kasar Senegal

People celebrating

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Magoya bayan Shugaba Macky Sall suna murnar samun nasararsa ranar Litinin bayan da sakamkon farko-farko suna nuna shi ke kan gaba

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya lashe zaben kasar da aka yi ranar Lahadi a karo na biyu, inda zai yi shekara bakwai a karagar mulki.

Ya yi nasara a zaben da kashi 58 cikin 100 inda ya fafata da mutum hudu, amma an zarge shi da hana wasu daga cikin abokan hamayyarsa tsayawa takara a zaben.

An hana wasu fitattun mutane tsayawa zaben saboda zarge-zargen cin hanci.

An fara zaben Mr Sall matsayin shugaban kasa ne a shekarar 2012. Ya yi ta yin alkawura gudanar da sabbin ayyuka na abubuwan more rayuwa a yayin neman zabensa.

Ya nuna kansa a matsayin mai son kawo sauye-sauye na zamani, al'amarin da ya bunkasa tattalin arzikin kasar da kashi 6 cikin 100 a shekara daya, daya daga cikin bunkasar da aka taba samu a Afirka.

Sai dai masu suka na cewa yawancin 'yan kasar ta Senegal ba su amfana da wadannan ayyuka ba.

Presentational grey line

Sakamakon zaben shugaban kasa:

  • Macky Sall: Kashi 58%
  • Idrissa Seck: Kashi 21%
  • Ousmane Sonko: Kashi 16%
  • El Hadj Issa Sall: Kashi 4%
  • Madické Niang: Kashi 1%
  • Adadin mutanen da suka kada kuri'a: Kashi 66%
Presentational grey line

Khalifa Sall (ba shi da alaka da shugaban kasar), fitaccen tsohon magajin garin Dakar, da Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar, ba su samu damar tsayawa takarar ba bayan da aka kama su da laifin cin hanci.

A sakamakon haka, babu daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa biyu na Socialist Party da Senegalese Democratic Party wadanda suka mamaye al'amuran siyasar kasar tun bayan samun 'yancin kai da suka gabatar da 'yan takararsu.

Daya abokin adawar Mr Sall tsohon Firai Ministan kasar Idrissa Seck, ya samu kashi 21% na kuri'un.

President Macky Sall greets the crowd as he speaks to the media after casting his vote

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Sall zai sake yin shekara bakwai a kan mulki

Baki daya dai, 'yan takara biyar ne aka sanya sunansu a takardar kada kuri'ar, ba kamar 1 ba a wancan zaben.

Fiye da mutum miliyan 6.6 ne suka yi rijista a zaben da aka gudanar ranar Lahadi, da suka hada da 'yan kasar mazauna kasashen waje, kuma kashi 66 cikin 100 suka kada kuri'unsu.